Sashe na 10: Hidima ta Baya a Pereya
Wataƙila daga Bikin Keɓewa a shekara ta 29 bayan haihuwar Almasihu zuwa tafiya ta ƙarshe a shekara ta 30 bayan haihuwar Almasihu (kimanin watanni uku da rabi)
Yesu Ya Ja Baya Zuwa Betani a Ɗaya Gefen Urdun
Yesu ya ja baya daga Urushalima zuwa Betani a ɗaya gefen Urdun.
Pereya
29 zuwa 30 bayan haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
Yohanna 10:40–42
10:40 Sa’an nan Yesu ya sāke koma ƙetaren Urdun inda dā Yohanna yake baftisma. A can ya zauna 41 mutane da yawa suka zo wurinsa. Suka ce, “Ko da yake Yohanna bai yi wani abin banmamaki ba, duk abubuwan da Yohanna ya faɗa game da mutumin nan gaskiya ne.” 42 A nan kuwa mutane da yawa suka gaskata da Yesu.
Yesu Ya Koyar a Pereya Kuma Aka Yi Masa Gargaɗi Game da Hiridus
Yesu ya koyar a Pereya, a kan tafiyarsa zuwa Urushalima, kuma aka yi masa gargaɗi game da Hiridus Antifas.
Luka 13:22–35
13:22 Sa’ad da Yesu yana kan hanyarsa zuwa Urushalima, sai ya bi ta cikin garuruwan da ƙauyukan, yana koyarwa. 23 Sai wani ya tambaye shi ya ce, “Ya Ubangiji, shin, wai mutane kima ne kawai za su sami ceto?”
Ya ce musu, 24 “Ku yi matuƙar ƙoƙari ku shiga ta matsattsiyar ƙofa, domin ina faɗa muku, mutane da yawa za su yi ƙoƙarin shiga, amma ba za su iya ba. 25 Da zaran maigidan ya tashi ya rufe ƙofar, za ku tsaya a waje kuna ƙwanƙwasawa, kuna roƙo cewa, ‘Ranka yă daɗe, buɗe mana ƙofa.’
“Amma shi zai amma ya ce, ‘Ni ban san ku, ko inda kuka fito ba.’
26 “Sa’an nan za ku ce, ‘Haba, mu da muka ci, muka sha tare da kai, har ka yi koyarwa a cikin titi-titi namu.’
27 “Amma shi zai amma ya ce, ‘Ban san ku, ko inda kuka fito ba. Ku rabu da ni, dukan ku masu aikata mugunta!’
28 “Za a yi kuka a can, da cizon haƙora, sa’ad da kuka ga Ibrahim, da Ishaku, da Yaƙub, da dukan annabawa a mulkin Allah, amma ku kuwa, za a jefar da ku a waje. 29 Mutane za su zo daga gabas, da yamma, da kudu, da arewa, su ɗauki wuraren zamansu a bikin, a cikin mulkin Allah. 30 Tabbatacce, akwai waɗansu da suke na ƙarshe, da za su zama na farko, na farko kuma, da za su zama na ƙarshe.”
31 A wannan lokaci, waɗansu Farisiyawa suka zo suka ce wa Yesu, “Ka bar nan ka tafi wani wuri dabam. Hiridus yana so ya kashe ka.”
32 Ya amsa ya ce, “Ku je ku gaya wa dilan nan, wato, mai makirci cewa, ‘Da yau da kuma gobe, zan fitar da aljanu, in kuma warkar da mutane, sa’an nan a rana ta uku in cika burin aikina. 33 Duk da haka, dole in ci gaba da aikin a yau, da kuma gobe, sa’an nan in ci gaba da yin haka kashegari kuma, gama tabbatacce, ba annabi da yakan mutu a bayan birnin Urushalima!’
34 “Urushalima, ayya Urushalima, ke da kika kashe annabawa, kuma kika jefa wa waɗanda aka aika gare ki da duwatsu. Sau da yawa na yi kewan in tattara ’ya’yanki wuri ɗaya, kamar yadda kaza takan tattara ’ya’yanta cikin fikafikanta, amma ba ki yarda ba! 35 Duba, an bar muku gidanku fanko. Ina kuwa faɗa muku, ba za ku sāke ganina ba, sai kun ce, ‘Mai albarka ne shi wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji.’ ”
Yayin Cin Abinci da Wani Babban Bafarisiye, Yesu Ya Sake Warkarwa
Yayin cin abinci (na safe) tare da wani babban Bafarisiye, Yesu ya sake warkarwa a ranar Asabbaci, ya kuma kāre kansa. Wannan yanayin ya ba da damar faɗin misalai uku.
Wataƙila a Pereya
Luka 14:1–24
14:1 Wata ranar Asabbaci, da Yesu ya shiga gidan wani sanannen Bafarisiye don cin abinci, sai mutane suka zuba masa ido da kyau. 2 A nan a gabansa kuwa akwai wani mutum mai ciwon kumburin ƙafa da hannu. 3 Sai Yesu ya tambayi masanan dokoki da Farisiyawa ya ce, “Daidai ne bisa ga doka, a yi warkarwa a ranar Asabbaci, ko babu?” 4 Amma ba su ce kome ba. Sai ya riƙe mutumin, ya warkar da shi, sa’an nan ya sallame shi.
5 Sai ya tambaye, su ya ce, “In wani a cikinku yana da ɗa, ko bijimi da ya faɗa a rijiya a ranar Asabbaci, ba za ku cire shi nan da nan ba?” 6 Suka rasa abin faɗi.
7 Da ya lura da yadda baƙi suna zaɓan wuraren zama masu bangirma a tebur, sai ya faɗa musu wannan misali, ya ce; 8 “In wani ya gayyace ka bikin aure, kada ka zaɓi wurin zama mai bangirma, don wataƙila akwai wani da ya fi ka girma, da aka gayyata. 9 In kuwa haka ne, wanda ya gayyace duk biyunku, zai zo ya ce maka, ‘Ka ba wa mutumin nan wurin zamanka.’ Ka ga, an ƙasƙantar da kai, kuma dole ka ɗauki wuri mafi ƙasƙanci. 10 Amma in an gayyace ka, ɗauki wuri mafi ƙasƙanci, don in wanda ya gayyace ka ya zo, zai ce maka, ‘Ka hawo nan aboki a wuri mafi girma.’ Wannan zai ɗaukaka ka a gaban dukan ’yan’uwanka baƙi. 11 Gama duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Shi wanda kuma ya ƙasƙantar da kansa, za a ɗaukaka shi.”
12 Sai Yesu ya ce wa wanda ya gayyace shi, “Lokacin da ka shirya biki ko liyafa, kada ka gayyaci abokanka, ko ’yan’uwanka, ko danginka, ko kuma maƙwabtanka masu arziki, gama in ka yi haka, suna iya gayyatarka, su biya maka alherin da ka yi musu. 13 Amma lokacin da ka kira biki, ka gayyaci matalauta, da guragu, da shanyayyu, da makafi. 14 Ta haka, za ka sami albarka. Ko da yake ba za su iya biyan ka ba, za a biya ka a ranar tashin masu adalci daga matattu.”
15 Da jin haka, sai wani da yake tare da shi a tebur ɗin, ya ce wa Yesu, “Mai albarka ne wanda zai ci abinci a bikin nan a mulkin Allah.”
16 Yesu ya amsa ya ce, “Wani mutum yana shirya wani babban biki, ya kuma gayyaci baƙi da yawa. 17 Da lokacin bikin ya yi, sai ya aiki bawansa ya je ya ce wa waɗanda aka gayyata, ‘Ku zo, don an shirya kome.’
18 “Amma sai dukansu suka fara ba da hujjoji. Na farkon ya ce, ‘Na sayi gona yanzun nan, dole in je in ga yadda take, ina roƙonka ka yi mini haƙuri.’
19 “Wani ya ce, ‘Na sayi shanun noma guda goma yanzun nan, ina kan hanyata ke nan in gwada su, ina roƙonka, ka yi mini haƙuri.’
20 “Har yanzu wani ya ce, ‘Na yi aure yanzun nan, don haka ni ba zan iya zuwa ba.’
21 “Bawansa ya dawo ya gaya wa maigidansa wannan. Sai maigidan ya yi fushi, ya ba da umarni ga bawansa ya ce, ‘Ka fita da sauri, ka bi titi-titi da lungu-lungu na garin, ka kawo matalauta, da guragu, da makafi, da shanyayyu.’
22 “Bawan ya dawo ya ce, ‘Ranka yă daɗe, an yi abin da ka umarta, amma har yanzu da sauran wuri.’
23 “Maigidan ya ce wa bawansa, ‘Ka je kan hanyoyin da layi-layi na karkara, ka sa su shigo, don gidana ya cika.’ 24 Ina gaya muku, babu ko ɗaya daga cikin mutanen nan da aka gayyata da zai ɗanɗana bikina.”