Sashe na 7: Babbar Hidima a Galili

Wataƙila daga kaka ta shekara ta 27 zuwa bazarar shekara ta 29 bayan haihuwar Kiristi (da alama kusan shekara ɗaya da rabi)

Markus ya ba da cikakken bayani sosai game da wannan lokaci, Luka kuma ya taƙaita labarin, amma Mattiyu ya fi tsara wannan sashe bisa jigogi. Bisharar Markus ta shiga Babbar Hidima a Galili kai tsaye (a kwatanta da taƙaitaccen bayanin da Bitrus ya yi wa iyalin Korneliyus game da rayuwar Kiristi a Ayyukan Manzanni 10:36–43). Yawan bayanan ya sa rarraba su a fili yake da wuya, amma abubuwan da suka faru suna ci gaba a jere.

  • An Ƙi Yesu a Nazaret, Ya Ƙaura Zuwa Kafarnahum
  • Zagaye na farko a Galili tare da masuntan nan huɗu, da kuma kiran Mattiyu (Lawi) a kan hanyar dawowa, yayin da sunan Yesu yake ƙara yaɗuwa.
  • Gardama Game da Asabbaci a Urushalima da Galili
  • Yesu Ya Zaɓi Sha Biyun Ya Kuma Yi Wa'azi a Kan Dutse
  • Tasirin Kiristi ya ƙaru, Yohanna kuma ya yi tambaya daga kurkuku
  • Yawon Galili na biyu (yanzu tare da sha biyun), da tsananin ƙiyayyar Farisiyawa.
  • Rukunin farko mai girma na misalai, tare da ziyarar zuwa Gerasa (Kursi) da ziyarar ƙarshe zuwa Nazaret.
  • Zagaye na uku a Galili (Yesu yana bin sha biyun a baya), da tasirinsa a kan Hiridus Antifas.

Yesu Yana Koyarwa a Galili

Bayani na gaba ɗaya game da koyarwar Yesu a Galili.

27 zuwa 29 bayan haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Mattiyu 4:17

4:17 Tun daga wannan lokaci, Yesu ya fara wa’azi yana cewa, “Ku tuba, gama mulkin sama ya yi kusa.”

Markus 1:15

1:15 Yana cewa, “Lokaci ya yi. Mulkin Allah ya yi kusa. Ku tuba, ku gaskata bishara!”

Luka 4:15

4:15 Ya yi ta koyarwa a majami’unsu, kowa kuwa ya yabe shi.

A Kana Yesu Ya Warkar da Ɗan Wani Jami'i

A Kana, Yesu ya warkar da ɗan wani jami'in sarki na Kafarnahum.

A nan, a labarin ƙin Yesu a Nazaret da sabon gidansa a Kafarnahum, Yesu ya sake ziyartar Kana da Nazaret, ya sake kiran masuntan nan huɗu a bakin Tekun Galili, ya kuma fara hidimarsa ta koyarwa da warkarwa a Kafarnahum.

Yohanna 4:46–54

4:46 Sai ya sāke ziyarci Kana ta Galili inda ya juya ruwa ya zama ruwan inabi. Akwai wani ma’aikacin hukuma a can wanda ɗansa yake kwance da rashin lafiya a Kafarnahum. 47 Da mutumin nan ya ji cewa Yesu ya isa Galili daga Yahudiya, sai ya je wurinsa ya roƙe shi yă zo yă warkar da ɗansa da yake bakin mutuwa.

48 Yesu ya ce masa, “Ku mutane, in ba kun ga alamu da abubuwan banmamaki ba, ba yadda za a yi ku ba da gaskiya.”

49 Ma’aikacin hukuman ya ce, “Ranka yă daɗe, ka zo kafin ɗana yă mutu.”

50 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ka tafi. Ɗanka zai rayu.”

Mutumin kuwa ya amince da maganar da Yesu ya yi ya kuwa tafi. 51 Tun yana kan hanya, bayinsa suka tarye shi da labari cewa yaron yana warkewa. 52 Da ya tambayi lokacin da ɗansa ya sami sauƙi, sai suka ce masa, “Zazzaɓin ya sake shi jiya a sa’a ta bakwai.”

53 Sai mahaifin ya gane a daidai wannan lokaci ne Yesu ya ce masa, “Ɗanka zai rayu.” Saboda haka shi da dukan iyalinsa suka gaskata.

54 Wannan ce abin banmamaki ta biyu da Yesu ya yi, bayan zuwansa daga Yahudiya zuwa Galili.

Nazaret Ta Ƙi Yesu a Karon Farko

Luka 4:16–31

4:16 Ya tafi Nazaret, inda aka yi renonsa. A ranar Asabbaci kuma, ya shiga majami’a kamar yadda ya saba. Sai ya miƙe don yă yi karatu. 17 Aka kuwa ba shi naɗaɗɗen littafin annabi Ishaya. Da ya buɗe, sai ya sami wurin da aka rubuta,

18 “Ruhun Ubangiji yana kaina,

domin ya shafe ni,

in yi wa matalauta wa’azin bishara.

Ya aiko ni in yi shelar ’yanci ga ’yan kurkuku,

in kuma buɗe idanun makafi,

in ba da ’yanci ga waɗanda aka danne.

19 In yi shelar shekarar tagomashin Ubangiji.”

20 Sai ya naɗe naɗaɗɗen littafin ya mayar wa mai hidimar, ya kuma zauna. Dukan idanun waɗanda suke a majami’ar, suka koma a kansa. 21 Sai ya fara ce musu, “A yau, Nassin nan, ya cika a kunnenku.”

22 Duk suka yabe shi, suka yi mamakin kalmomin alheri da suke fitowa daga bakinsa. Suka yi tambaya, suna cewa, “Anya, wannan ba ɗan Yusuf ba ne?”

23 Yesu ya ce musu, “Tabbatacce, na san za ku faɗa mini karin maganan nan, ‘Likita, warkar da kanka! Ka kuma yi abin da muka ji ka yi a Kafarnahum, a nan garinka.’ ”

24 Ya ci gaba, da ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, babu annabin da ake yarda da shi a garinsa. 25 Ina tabbatar muku a zamanin Iliya, akwai gwauraye da yawa a Isra’ila, sa’ad da aka rufe sararin sama har shekara uku da rabi, aka kuma yi yunwa mai tsanani ko’ina a ƙasar. 26 Duk da haka, ba a aiki Iliya ga ko ɗaya a cikinsu ba. Sai dai zuwa ga wata gwauruwa da take a Zarefat, a yankin Sidon. 27 Akwai kuma mutane da yawa a Isra’ila masu kuturta a zamanin annabi Elisha, amma ba ko ɗayansu da aka tsarkake sai Na’aman mutumin Suriyan nan kaɗai.”

28 Dukan mutanen da suke cikin majami’a suka fusata ƙwarai da jin wannan. 29 Suka tashi, suka fitar da Yesu bayan gari, suka kai shi goshin tudun da aka gina garin, don su ture shi ƙasa, 30 amma sai ya bi ta tsakiyar taron ya yi tafiyarsa.

31 Sai ya tafi Kafarnahum, wani gari a Galili, a ranar Asabbaci kuma, ya fara koya wa mutane.

Yesu Ya Kafa Gidansa a Kafarnahum

Mattiyu 4:13–16

4:13 Ya bar Nazaret, ya je ya zauna a Kafarnahum, wadda take a bakin tafki wajen Zebulun da Naftali 14 don a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya cewa,

15 “Ƙasar Zebulun da ƙasar Naftali,

da kuke a hanyar zuwa tekun Galili, a ƙetaren Urdun,

wannan yankin Galili ta Al’ummai,

16 mutanen da suke zama cikin duhu

sun ga babban haske;

haske kuma ya haskaka

a kan waɗanda suke zama a inuwar mutuwa.”