Annas Ne Ya Fara Yi wa Yesu Tambayoyi
Annas, tsohon babban firist, ne ya fara yi wa Yesu tambayoyi.
Juma'a kafin wayewar gari
Shari'ar da Yahudawa suka yi, da abubuwan da suka faru dangane da ita.
30 ko 29 bayan haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
Yohanna 18:13–14, 19–23
18:13 sa’an nan suka kawo shi da farko wurin Annas, wanda yake surukin Kayifas, babban firist a shekaran nan. 14 Kayifas ne wanda ya shawarci Yahudawa cewa zai fi kyau mutum ɗaya yă mutu saboda mutane.
19 Ana cikin haka, sai babban firist ya tuhumi Yesu game da almajiransa da kuma koyarwarsa.
20 Yesu ya amsa ya ce, “Ai, na yi wa duniya magana a fili. Na kuma sha yin koyarwa a majami’u ko kuma a haikali inda Yahudawa duka sukan taru. Ban taɓa faɗin kome a ɓoye ba. 21 Don me kake tuhumata? Ka tambayi waɗanda suka ji ni. Ba shakka, sun san abin da na faɗa.”
22 Da Yesu ya faɗa haka, sai ɗaya daga cikin ma’aikatan da yake tsaye kusa ya mare shi a fuska ya ce, “Haka za ka amsa wa babban firist?”
23 Yesu ya amsa ya ce, “In na faɗi abin da ba daidai ba, ka nuna abin da ba daidai ba. Amma in gaskiya na faɗa, don me ka mare ni?”
Kayifas da Majalisa Sun Yanke wa Yesu Hukunci
Kayifas da Majalisa sun yi wa Yesu shari'a cikin gaggawa suka yanke masa hukunci, suka yi masa ba'a, suka kuma buge shi.
Gidan babban firist Kayifas. Kafin wayewar gari ranar Juma'a
Mattiyu 26:57, 59–68
26:57 Waɗanda suka kama Yesu kuwa suka kai shi wurin Kayifas, babban firist, inda malaman dokoki da dattawa suka taru.
59 Sai manyan firistoci da ’yan majalisa duka suka yi ta neman shaidar ƙarya a kan Yesu, don su sami dama su kashe shi.
60 Amma ba su sami ko ɗaya ba, ko da yake masu shaidar ƙarya da yawa sun firfito.
A ƙarshe, biyu suka zo gaba,
61 suka furta cewa, “Wannan mutum ya ce, ‘Ina iya rushe haikalin Allah, in sāke gina shi cikin kwana uku.’ ”
62 Sa’an nan babban firist ya miƙe tsaye, ya ce wa Yesu, “Ba ka da wata amsa? Shaidar da mutanen nan suke yi a kanka fa?”
63 Amma Yesu ya yi shiru.
Sai babban firist ya ce masa, “Na haɗa ka da Allah mai rai. Faɗa mana in kai ne Kiristi, Ɗan Allah.”
64 Sai Yesu ya amsa ya ce, “I, haka yake yadda ka faɗa. Sai dai ina gaya muku duka, nan gaba, za ku ga Ɗan Mutum zaune a hannun dama na Mai Iko, yana kuma zuwa a kan gizagizan sama.”
65 Sa’an nan babban firist ya yage tufafinsa ya ce, “Ya yi saɓo! Don me muke bukatar ƙarin shaidu? Ga shi, yanzu kun dai ji saɓon.
66 Me kuka gani?”
Suka amsa, suka ce, “Ya cancanci mutuwa.”
67 Sai suka tottofa masa miyau a fuskarsa, suka kuma bubbuge shi da hannuwansu. Waɗansu kuma suka mammare shi
68 suka ce, “Yi mana annabci, Kiristi. Wa ya buge ka?”
Markus 14:53, 55–65
14:53 Suka kai Yesu wajen babban firist, sai dukan manyan firistoci, dattawa da kuma malaman dokoki suka taru.
55 Manyan firistoci da dukan ’yan Majalisa, suka shiga neman shaidar laifin da za a tabbatar a kan Yesu, domin su kashe shi. Amma ba su sami ko ɗaya ba.
56 Da yawa suka ba da shaidar ƙarya a kansa, amma shaidarsu ba tă zo ɗaya ba.
57 Sai waɗansu suka miƙe tsaye, suka ba da wannan shaida ƙarya a kansa, suka ce,
58 “Mun ji shi ya ce, ‘Zan rushe wannan haikali da mutum ya gina, cikin kwana uku, in sāke gina wani wanda ba ginin mutum ba.’ ” 59 Duk da haka ma, shaidarsu ba tă zo ɗaya ba.
60 Sai babban firist ya tashi a gabansu, ya tambayi Yesu ya ce, “Ba za ka amsa ba? Wane shaida ke nan waɗannan mutane suke kawowa a kanka?”
61 Amma Yesu ya yi shiru, bai kuwa amsa ba.
Babban firist ya sāke tambayarsa ya ce, “Kai ne Kiristi, Ɗan Mai Albarka?”
62 Yesu ya ce, “Ni ne. Za ku kuwa ga Ɗan Mutum yana zaune a hannun dama na Mai Iko, yana kuma zuwa a cikin gizagizan sama.”
63 Babban firist ya yage tufafinsa, ya yi ce, “Ina dalilin neman waɗansu shaidu kuma? 64 Kun dai ji saɓon. Me kuka gani?”
Duka suka yanke masa hukuncin kisa.
65 Sai waɗansu suka fara tattofa masa miyau, suka rufe masa idanu, suka bubbuge shi da hannuwansu, suka ce, “Yi annabci!” Masu gadin kuma suka ɗauke shi, suka yi masa duka.
Luka 22:54, 63–65
22:54 Sai suka kama shi suka kai shi gidan babban firist. Bitrus ya bi su daga nesa.
63 Mutanen da suke gadin Yesu suka fara masa ba’a da dūka.
64 Suka rufe masa idanu suna tambaya cewa, “Ka yi annabci! Wa ya mare ka?”
65 Suka kuma yi masa waɗansu baƙaƙen maganganu masu yawa.
Yohanna 18:24
18:24 Sai Annas ya aika da shi, a daure, wurin Kayifas babban firist.