Sashe na 11: Hidimar Ƙarshe a Gaban Jama'a a Urushalima

Daga Juma'ar da ke gaban Makon Wahala zuwa Talatar makon, a bazarar shekara ta 30 Miladiyya (ko 29 Miladiyya). Jim kaɗan kafin Ƙetarewa

Yesu Ya Isa Betani Kusa da Urushalima

Juma'a da rana

30 ko 29 bayan haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Yohanna 11:55–12:1, 9–11

11:55 Sa’ad da lokaci ya yi kusa a yi Bikin Ƙetarewa na Yahudawa, da yawa suka haura daga ƙauyuka zuwa Urushalima, don su tsarkake kansu kafin Bikin Ƙetarewa. 56 Suka yi ta neman Yesu, da suke a tsaitsaye a filin haikali kuwa suka dinga tambayar juna, suna cewa, “Me kuka gani? Anya, zai zo Bikin kuwa?” 57 Manyan firistoci da Farisiyawa tuni sun riga sun yi umarni cewa duk wanda ya san inda Yesu yake, yă faɗa don su kama shi.

12:1 Kwana shida kafin Bikin Ƙetarewa, sai Yesu ya iso Betani, inda Lazarus yake, wanda Yesu ya tā da daga matattu.

9 Ana cikin haka sai babban taron Yahudawa suka sami labari Yesu yana can suka kuwa zo, ba kawai don shi ba amma don su kuma ga Lazarus, wanda ya tā da daga matattu. 10 Saboda haka manyan firistoci suka ƙulla su kashe Lazarus shi ma, 11 gama dalilinsa Yahudawa da yawa suna komawa ga Yesu suna kuma ba da gaskiya gare shi.

Yesu Ya Shiga Urushalima Cikin Nasara a Matsayin Almasihu

A nan muna da tafiye-tafiye da koyarwar Mai Ceto a ranar Lahadi, Litinin, da Talata: ƙarshen hidimarsa a gaban jama'a, ban da ɗan abin da ya faɗa a lokacin shari'o'insa a gaban Yahudawa da Romawa. Dukan koyarwarsa bayan wannan ga almajiransa yake yi.

Daga Betani zuwa Urushalima da komowa (Lahadi). Ranar bayyana kansa a matsayin Almasihu

Mattiyu 21:1–3, 6–7, 4–5, 8–11, 14–17

21:1 Da suka yi kusa da Urushalima suka kuma kai Betfaji da yake kan Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki almajirai biyu,

2 yana ce musu, “Ku je ƙauyen da yake gabanku, nan take za ku ga wata jaka a daure tare da ɗanta kusa da ita, a can. Ku kunce su ku kawo mini.

3 In wani ya yi muku wata magana, ku ce masa Ubangiji yana bukatarsu, zai kuwa mai da su nan da nan.”

6 Almajiran suka tafi suka yi kamar yadda Yesu ya umarce su.

7 Suka kawo jakar da ɗanta, suka shimfiɗa mayafansu a kansu, Yesu kuma ya zauna a kansu.

4 Wannan ya faru ne don a cika abin da aka faɗa ta bakin annabin cewa,

5 “Ku ce wa Diyar Sihiyona,

‘Duba, sarkinki yana zuwa gare ki,

mai tawali’u yana a kan jaki,

a kan aholaki, ɗan jaki.’ ”

8 Wani babban taron mutane suka shimfiɗa mayafansu a kan hanya, yayinda waɗansu suka sassari rassan itatuwa suka shisshimfiɗa a kan hanya.

9 Taron mutanen da suke gabansa da kuma waɗanda suke binsa a baya suka yi ihu suna cewa,

“Hosanna ga Ɗan Dawuda!”

“Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!”

“Hosanna a cikin sama!”

10 Sa’ad da Yesu ya shiga Urushalima, dukan birnin ya ruɗe, ana ta tambaya, “Wane ne wannan?”

11 Taron mutane suka amsa, “Wannan shi ne Yesu, annabin nan daga Nazaret a Galili.”

14 Makafi da guragu suka zo wurinsa a haikali, ya kuwa warkar da su.

15 Amma da manyan firistoci da malaman dokoki suka ga abubuwan banmamakin da ya yi, yara kuma suna ihu a filin haikali suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda,” sai fushi ya kama su.

16 Suka tambaye shi suka ce, “Kana jin abin da waɗannan suke faɗa?”

Yesu ya amsa ya ce, “I, ba ku taɓa karanta ba cewa,

“ ‘Daga leɓunan yara da jarirai

kai, Ubangiji, ka shirya wa kanka yabo’?”

17 Sai ya bar su, ya fita daga birnin ya tafi Betani, inda ya kwana.

Markus 11:1–11

11:1 Sa’ad da suka yi kusa da Urushalima, suka zo Betfaji da Betani wajen Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki biyu daga cikin almajiransa,

2 ya ce musu, “Ku je ƙauyen da yake gaba da ku, da shigarku, za ku tarar da wani ɗan jaki a daure a can, wanda ba wanda ya taɓa hawa. Ku kunce shi ku kawo nan.

3 In wani ya tambaye ku, ‘Don me kuke yin haka?’ Ku gaya masa cewa, ‘Ubangiji yana bukatarsa, zai kuma dawo da shi ba da jimawa ba.’ ”

4 Suka tafi, suka kuwa tarar da wani ɗan jaki a waje, a titi, daure a ƙofar gida. Suna cikin kunce shi ke nan,

5 sai waɗansu mutane da suke tsattsaye a wurin suka ce musu, “Me kuke yi da kuke kunce ɗan jakin nan?”

6 Suka amsa kamar yadda Yesu ya ce su yi. Mutanen kuwa suka ƙyale su.

7 Da suka kawo shi wajen Yesu, sai suka shimfiɗa rigunarsu a bayansa. Yesu kuwa ya hau ya zauna bisansa.

8 Mutane da yawa suka shimfiɗa rigunarsu a kan hanya, waɗansu kuma suka baza rassan itatuwan da suka sara daga gonaki. 9 Waɗanda suka yi gaba, da kuma waɗanda suke biye, duk suka ɗaga murya, suna cewa,

“Hosanna!”

“Mai albarka ne wanda yake zuwa a cikin sunan Ubangiji!”

10 “Mai albarka ne mulkin nan mai zuwa na mahaifinmu Dawuda!”

“Hosanna a can cikin samaniya!”

11 Yesu ya shiga Urushalima ya kuma tafi filin haikali. Ya dudduba kome duka, amma da yake yamma ta yi, sai ya tafi Betani tare da Sha Biyun.

Luka 19:29–44

19:29 Da ya kai kusa da Betfaji da Betani, a tudun da ake kira Dutsen Zaitun, sai ya aiki almajiransa guda biyu, ya ce musu,

30 “Ku je ƙauyen da yake gaba da ku. Da kuna shiga, za ku tarar da wani ɗan jaki, wadda ba wanda ya taɓa hawa, a daure a wurin. Ku kunce shi ku kawo nan.

31 In wani ya tambaye ku, ‘Don me kuke kunce shi?’ Ku ce masa, ‘Ubangiji yana bukatarsa.’ ”

32 Waɗanda aka aika su yi gaba suka tafi, suka kuwa tarar kamar yadda ya gaya musu.

33 Suna cikin kunce ɗan jakin, sai masu ɗan jakin suka ce musu, “Don me kuke kunce shi?”

34 Suka amsa suka ce, “Ubangiji ne na bukatarsa.”

35 Suka kawo shi wurin Yesu. Suka sa rigunarsu a kan ɗan jakin, sa’an nan suka sa Yesu a kai.

36 Yana cikin tafiya, sai mutane suka shimfiɗa rigunarsu a kan hanya.

37 Da ya yi kusa da wurin da hanyar ta gangara zuwa Dutsen Zaitun, sai dukan taron almajirai suka fara yabon Allah, da muryoyi masu ƙarfi, da murna, saboda dukan ayyukan banmamaki da suka gani. Suna cewa,

38 “Mai albarka ne sarki wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!”

“Salama ta kasance a sama, da ɗaukaka kuma a can cikin sama!”

39 Sai waɗansu Farisiyawa a cikin taron suka ce wa Yesu, “Malam, ka kwaɓi almajiranka!”

40 Ya amsa ya ce, “Ina gaya muku, ko da sun yi shiru, duwatsu za su fara kirari.”

41 Da ya yi kusa da Urushalima, ya kuma ga birnin, sai ya yi kuka a kanta, 42 kuma ya ce, “In ke, ko ke ɗin ma, dā ma kin san abin da zai kawo miki salama a wannan rana, amma yanzu an ɓoye shi daga idanunki. 43 Ranakun za su auko miki, a lokacin da abokan gābanki za su gina bango gāba da ke, su kuma kewaye inda kike, za su kuma tsare kowane gefenki, su sa ke a tsakiya. 44 Za su fyaɗa ke a ƙasa, ke da ’ya’yan da suke cikin katanganki. Ba za su bar wani dutse a kan wani ba, saboda ba ki gane da lokacin da Allah zai ziyarce ki ba.”

Yohanna 12:12–19

12:12 Kashegari babban taron da suka zo Bikin suka sami labari cewa Yesu yana kan hanyarsa zuwa Urushalima.

13 Sai suka ɗaɗɗauko rassan dabino suka fiffita taryensa, suna ɗaga murya suna cewa,

“Hosanna!”

“Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!”

“Mai albarka ne Sarkin Isra’ila!”

14 Yesu ya sami ɗan jaki, ya hau, kamar yadda yake a rubuce cewa,

15 “Kada ki ji tsoro, ya Diyar Sihiyona;

duba, ga sarkinki yana zuwa,

zaune a kan aholaki jaki.”

16 Da fari almajiransa ba su gane dukan wannan ba. Sai bayan da aka ɗaukaka Yesu, sa’an nan suka gane cewa an rubuta waɗannan abubuwa game da shi ne, har ma suka yi masa waɗannan abubuwa.

17 Taron da suke tare da shi a sa’ad da ya kira Lazarus daga kabari ya kuma tā da shi daga matattu suka yi ta baza labarin.

18 Mutane da yawa kuwa suka fita taryensa, saboda sun ji labarin abin banmamakin da ya yi.

19 Saboda haka Farisiyawa suka ce wa juna, “Duba, wannan ba ya kai mu ko’ina. Ga shi, duk duniya tana bin sa!”