Yesu Ya Bayyana ga Almajirai Bakwai a Gefen Tekun Galili
Yesu ya bayyana ga almajirai bakwai a gefen Tekun Galili. Kamun kifi ta mu'ujiza.
30 ko 29 bayan haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
Yohanna 21:1–25
21:1 Daga baya Yesu ya sāke bayyana kansa ga almajiransa, a bakin Tekun Tibariya. Ga yadda ya faru. 2 Siman Bitrus, Toma (wanda ake kira Didaimus), Natanayel daga Kana ta Galili, ’ya’yan Zebedi maza, da kuma waɗansu almajirai guda biyu suna tare. 3 Sai Siman Bitrus ya ce musu, “Za ni kamun kifi,” suka ce, “Za mu tafi tare da kai.” Saboda haka suka fita suka shiga jirgin ruwa, amma a daren nan ba su kama kome ba.
4 Da sassafe, sai ga Yesu tsaye a gaci, amma almajiran ba su gane cewa Yesu ne ba.
5 Sai ya ce musu, “Abokai, kuna da kifi kuwa?”
Suka amsa suka ce, “A’a.”
6 Ya ce musu, “Ku jefa abin kamun kifinku dama da jirgin ruwan, za ku samu.” Da suka yi haka, sai suka kāsa jawo abin kamun kifin saboda yawan kifi.
7 Sai almajirin da Yesu yake ƙauna ya ce wa Bitrus, “Ai, Ubangiji ne!” Nan da nan da Siman Bitrus ya ji ya ce, “Ai, Ubangiji ne,” sai ya yafa mayafinsa (don dā ma ya tuɓe shi), ya fāɗa cikin ruwan. 8 Sauran almajiran kuwa suka bi shi cikin jirgin ruwan, janye da abin kamun kifin cike da kifi, don ba su da nisa daga gaci, wajen yadi ɗari ne. 9 Da suka sauka, sai suka ga garwashin wuta a can da kifi a kai, da kuma ’yan burodi.
10 Yesu ya ce musu, “Ku kawo waɗansu kifin da kuka kama yanzu.” 11 Sai Siman Bitrus ya hau ya jawo abin kamun kifin gaci. Ya cika da manyan kifi, 153, amma duk da yawansun nan abin kamun kifin bai tsintsinke ba. 12 Yesu ya ce musu, “Ku zo ku karya kumallo.” Ba wani daga cikin almajiran da ya yi karambanin tambayarsa, “Wane ne kai?” Sun san cewa Ubangiji ne. 13 Yesu ya zo, ya ɗauki burodin ya ba su, haka kuma kifin. 14 Wannan fa shi ne sau na uku da Yesu ya bayyana kansa ga almajiransa bayan an tashe shi daga matattu.
15 Da suka gama ci, sai Yesu ya ce wa Siman Bitrus, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata da gaske fiye da waɗannan?”
Ya ce, “I, Ubangiji, ka san cewa ina sonka.”
Yesu ya ce, “Ciyar da ’ya’yan tumakina.”
16 Har wa yau Yesu ya ce, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata da gaske?”
Ya amsa ya ce, “I, Ubangiji, ka san cewa ina sonka.”
Yesu ya ce, “Lura da tumakina.”
17 Sau na uku ya ce masa, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata?”
Sai Bitrus ya ɓata rai saboda Yesu ya tambaye shi sau na uku, “Kana ƙaunata?” Ya ce, “Ubangiji ka san kome duka; ka san cewa, ina ƙaunarka.”
Yesu ya ce, “Ciyar da tumakina. 18 Gaskiya nake faɗa maka, sa’ad da kake saurayi kakan yi wa kanka sutura ka tafi inda ka so; amma sa’ad da ka tsufa za ka miƙa hannuwanka, wani dabam yă yi maka sutura yă kai ka inda ba ka so.” 19 Yesu ya faɗi wannan ne, don yă nuna irin mutuwar da Bitrus zai yi yă ɗaukaka Allah. Sa’an nan ya ce masa, “Bi ni!”
20 Bitrus ya juya ya ga cewa almajirin nan da Yesu yake ƙauna yana binsu. (Wannan ne ya jingina a jikin Yesu sa’ad da suke cin abincin yamman nan da ya ce, “Ubangiji wane ne zai bashe ka?”) 21 Da Bitrus ya gan shi sai ya ce, “Ubangiji, wannan fa?”
22 Yesu ya amsa ya ce, “Idan na so yă kasance da rai har in dawo, mene ne naka a ciki? Kai dai bi ni.” 23 Saboda wannan, jita-jita ta bazu a cikin ’yan’uwa cewa wannan almajirin ba zai mutu ba. Amma fa Yesu bai ce ba zai mutu ba; shi dai ya ce, “In na so yă kasance da rai har in dawo, mene ne naka a ciki?”
24 Wannan shi ne almajirin da ya ba da shaida a kan waɗannan abubuwa ya kuma rubuta su. Mun san cewa shaidarsa gaskiya ce.
25 Yesu ya yi waɗansu abubuwa da yawa kuma. Da a ce an rubuta kowannensu, na tabbata ko duniya duka ba za tă sami wuri saboda littattafan da za a rubuta ba.
Yesu Ya Bayyana ga Fiye da Mutum Ɗari Biyar a Galili
Yesu ya bayyana ga fiye da mutum ɗari biyar a kan wani dutsen da aka ƙayyade a Galili, kuma ya ba su aikin yi.
Mattiyu 28:16–20
28:16 Sa’an nan almajiransa goma sha ɗaya, suka tafi Galili, suka je dutsen da Yesu ya gaya musu. 17 Da suka gan shi, sai suka yi masa sujada, amma waɗansu suka yi shakka. 18 Sai Yesu ya zo wurinsu ya ce, “An ba ni dukan iko a sama da kuma ƙasa.
19 Saboda haka ku tafi, ku mai da dukan al’umman duniya su zama almajiraina, kuna yi musu baftisma a cikin sunan Uba, da na Ɗa, da na Ruhu Mai Tsarki, 20 kuna kuma koya musu, su yi biyayya da duk abin da na umarce ku, kuma tabbatacce, ina tare da ku kullum, har ƙarshen zamani.”
Markus 16:15–18
16:15 Ya ce, musu, “Ku tafi cikin dukan duniya, ku yi wa’azin bishara ga dukan halitta. 16 Duk wanda ya gaskata, aka kuma yi masa baftisma, zai sami ceto. Amma duk wanda bai gaskata ba kuwa, zai hallaka. 17 Waɗannan alamu za su kasance tare da waɗanda suka gaskata. A cikin sunana za su fitar da aljanu, za su yi magana da sababbin harsuna. 18 Za su ɗauki macizai da hannuwansu. In kuwa suka sha mugun dafi, ba zai cuce su ba ko kaɗan. Za su ɗibiya hannuwansu a kan marasa lafiya, su kuwa warke.”
Yesu Ya Ba Almajiran Wani Ƙarin Aiki
Yesu ya bayyana ga almajiran, ya kuma ba su wani ƙarin aiki.
Urushalima
Luka 24:44–49
24:44 Ya ce musu, “Wannan shi ne abin da na gaya muku tun ina tare da ku cewa, dole a cika kome da aka rubuta game da ni, a cikin Dokar Musa, da Annabawa, da kuma Zabura.”
45 Sai ya wayar da tunaninsu don su fahimci Nassi. 46 Ya ce musu, “Wannan shi ne abin da aka rubuta, cewa dole Kiristi yă sha wahala, a rana ta uku kuma yă tashi daga matattu. 47 Kuma a cikin sunansa za a yi wa’azin tuba da gafarar zunubai, ga dukan ƙasashe. Za a kuwa fara daga Urushalima. 48 Ku ne shaidun waɗannan abubuwa. 49 Zan aika muku da abin da Ubana ya yi alkawari. Amma ku dakata a birnin tukuna, sai an rufe ku da iko daga sama.”
Bayyanar Ƙarshe da Hawan Sama
A kan Dutsen Zaitun, tsakanin Urushalima da Betani
Markus 16:19–20
16:19 Bayan Ubangiji Yesu ya yi musu magana, sai aka ɗauke shi zuwa sama, ya kuma zauna a hannun dama na Allah. 20 Sai almajiran suka fita, suka yi wa’azi ko’ina. Ubangiji kuwa ya yi aiki tare da su, ya tabbatar da maganarsa ta wurin alamu da suke biye da maganar.
Luka 24:50–53
24:50 Bayan ya kai su waje kusa da Betani, sai ya ɗaga hannuwansa ya sa musu albarka.
51 Yana cikin sa musu albarka, sai ya rabu da su. Aka ɗauke shi zuwa cikin sama. 52 Sai suka yi masa sujada, suka koma Urushalima cike da murna sosai. 53 Sai suka ci gaba da zama a cikin haikalin, suna yabon Allah.