Sashe na 6: Mutuwar Yaƙub da Kakannin Al’umma

Yaƙub Ya Albarkaci ’Ya’yansa Maza Ya Kuma Mutu

1689 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Farawa 47:27–49:33

27 To, Isra’ilawa suka zauna a Masar a yankin Goshen. Suka mallaki filaye a can, suka riɓaɓɓanya suka ƙaru ƙwarai.

28 Yaƙub ya yi zama a Masar shekaru goma sha bakwai, yawan shekarunsa duka sun zama ɗari da arba’in da bakwai. 29 Sa’ad da lokaci ya gabato da Isra’ila zai mutu, sai ya kira ɗansa Yusuf, ya ce masa, “Ka yi mini wannan alheri, ka sa hannunka ƙarƙashin cinyar ƙafata, ka yi mini alkawari saboda ina roƙonka kaɗa ka bizne ni a Masar, 30 amma sa’ad da na huta da kakannina, ka ɗauke ni, ka fid da ni daga Masar, ka binne ni a inda aka binne su.”

Yusuf ya ce, “Zan yi yadda ka faɗa.”

31 Yaƙub ya ce, “Ka rantse mini.” Sai Yusuf ya rantse masa, Isra’ila kuwa ya yi godiya ga Allah yayinda ya jingina a kan sandansa.

48:1 Bayan wani lokaci aka faɗa wa Yusuf, “Mahaifinka yana ciwo.” Sai ya ɗauki ’ya’yansa maza biyu, Manasse da Efraim suka tafi tare da shi. 2 Sa’ad da aka faɗa wa Yaƙub, “Ɗanka Yusuf ya zo gare ka,” sai Isra’ila ya ƙoƙarta ya tashi ya zauna a kan gado.

3 Yaƙub ya ce wa Yusuf, “Allah Maɗaukaki ya bayyana gare ni a Luz a ƙasar Kan’ana, a can ya albarkace ni 4 ya kuma ce mini, ‘Zan sa ka yi ta haihuwa ka kuma riɓaɓɓanya, za ka ƙaru a yawa. Zan mai da kai al’ummar mutane, zan kuma ba ka wannan ƙasa tă zama madawwamiyar mallaka ga zuriyarka a bayanka.’

5 “To, yanzu, ’ya’ya mazanka biyu da aka haifa maka a Masar kafin in zo a nan za su zama nawa; Efraim da Manasse za su zama nawa, kamar yadda Ruben da Simeyon suke nawa. 6 Duk waɗansu ’ya’yan da aka haifa maka bayansu za su zama naka; a yankin da suka gāda za a lissafa a ƙarƙashin sunayen ’yan’uwansu. 7 Yayinda nake dawowa daga Faddan Aram, cikin baƙin cikina Rahila ta rasu a ƙasar Kan’ana yayinda muke kan hanya, ’yar rata daga Efrata. Saboda haka na binne ta a can kusa da hanya zuwa Efrata” (wato, Betlehem).

8 Sa’ad da Isra’ila ya ga ’ya’yan Yusuf maza, sai ya yi tambaya, “Su wane ne waɗannan?”

9 Yusuf ya ce wa mahaifinsa, “Su ne ’ya’yan da Allah ya ba ni a nan.”

Sa’an nan Isra’ila ya ce, “Kawo mini su saboda in albarkace su.”

10 Yanzu fa idanun Isra’ila sun fara rasa ƙarfi saboda tsufa, har ba ya iya gani sosai. Saboda haka Yusuf ya kawo ’ya’yansa maza kusa da shi, sai mahaifinsa ya sumbace su ya rungume su.

11 Isra’ila ya ce wa Yusuf, “Ban yi tsammani zan ga fuskarka kuma ba, yanzu kuwa Allah ya bar ni in ga ’ya’yanka su ma.”

12 Sa’an nan Yusuf ya ɗauke su daga gwiwoyin Isra’ila ya rusuna da fuskarsa har ƙasa. 13 Yusuf ya ɗauke su biyu, Efraim a damansa zuwa hagun Isra’ila, Manasse kuma a hagunsa zuwa hannun daman Isra’ila, ya kuma kawo su kusa da shi. 14 Amma Isra’ila ya miƙa hannun damansa ya sa shi a kan Efraim, ko da yake shi ne ƙaramin, ta wurin harɗewa hannuwansa, ya sa hannun hagunsa a kan Manasse, ko da yake Manasse ne ɗan farinsa.

15 Sa’an nan ya albarkaci Yusuf ya ce,

“Bari Allah a gaban wanda kakannina

Ibrahim da Ishaku suka yi tafiya,

Allahn da ya zama makiyayina

dukan raina zuwa wannan rana,

16 Mala’ikan da ya cece ni daga dukan cuta

bari yă albarkaci samarin nan.

Bari a kira su da sunana

da sunayen kakannina Ibrahim da Ishaku

bari kuma su ƙaru ƙwarai

a bisa duniya.”

17 Sa’ad da Yusuf ya ga mahaifinsa yana sa hannun damansa a kan Efraim bai ji daɗi ba; saboda haka ya ɗauke hannun mahaifinsa ya cire shi daga kan Efraim zuwa kan Manasse. 18 Yusuf ya ce masa, “A’a, mahaifina, wannan shi ne ɗan farin; ka sa hannunka na dama a kansa.”

19 Amma mahaifinsa ya ƙi ya ce, “Na sani, ɗana, na sani. Shi ma zai zama mutane, zai kuma zama mai girma. Duk da haka ɗan’uwansa zai zama mai girma fiye da shi, kuma zuriyarsa za tă zama ƙungiyar al’ummai.” 20 Ya albarkace su a wannan rana ya ce,

“A cikin sunanku Isra’ila zai sa wannan albarka

‘Bari Allah yă sa ku zama kamar Efraim da Manasse.’ ”

Saboda haka ya sa Efraim gaban Manasse.

21 Sa’an nan Isra’ila ya ce wa Yusuf, “Ina gab da mutuwa, amma Allah zai kasance tare da ku 22 Kuma gare ka, a matsayi wanda yake kan ’yan’uwanka, na ba da gonar da na karɓe daga Amoriyawa da takobi da kuma bakana.”

49:1 Sai Yaƙub ya kira ’ya’yansa maza ya ce, “Ku tattaru don in faɗa muku abin da zai faru gare ku, a kwanaki masu zuwa.

2 “Ku tattaru, ku saurara, ’ya’yan Yaƙub maza;

ku saurari mahaifinku, Isra’ila.

3 “Ruben, kai ne ɗan farina,

ƙarfina, alamar farko ta ƙarfina,

mafi matsayi, kuma mafi iko.

4 Mai tumbatsa kamar ruwa, amma ba za ka ƙara zama mai daraja ba,

gama ka hau gadon mahaifinka

ka hau kujerata, ka kuma ƙazantar da shi.

5 “Simeyon da Lawi ’yan’uwa ne,

takubansu makamai ne na tā da hankali.

6 Ba zan shiga shawararsu ba,

ba zan shiga taronsu ba,

gama sun kashe maza cikin fushinsu

cikin ganin dama suka kashe bijimai.

7 La’ananne ne fushinsu, mai tsanani ne ƙwarai,

hasalarsu kuwa, muguwa ce ƙwarai!

Zan warwatsa su cikin Yaƙub

in kuma daidaita su cikin Isra’ila.

8 “Yahuda, ’yan’uwanka za su yabe ka;

hannuwanka za su kasance a wuyan abokan gābanka,

’ya’yan mahaifinka maza za su rusuna maka.

9 Kai ɗan zaki ne, ya Yahuda,

ka dawo daga farauta, ɗana.

Kamar zaki, yakan kwanta a miƙe,

kamar zakanya, wa yake da ƙarfin halin tashe shi?

10 Kursiyi ba zai tashi daga Yahuda ba,

ba kuwa sandan mulki daga tsakani ƙafafunsa ba,

sai ya zo ga wanda yake mai shi.

Biyayyar al’umma kuwa tasa ce.

11 Zai daure jakinsa a kuringa,

aholakinsa a rassa mafi kyau;

zai wanke tufafinsa cikin ruwan inabi

rigunansa cikin inabi ja wur kamar jini.

12 Idanunsa za su duhunce fiye da ruwan inabi,

haƙorarsa farare kamar madara.

13 “Zebulun zai zauna a bakin teku,

yă zama tasar jiragen ruwa;

iyakarsa za tă nausa zuwa Sidon.

14 “Issakar doki mai ƙarfi,

kwance tsakanin buhunan sirdi.

15 Sa’ad da ya ga yadda wurin hutunsa yana da kyau

da kuma daɗin da ƙasarsa take,

zan tanƙware kafaɗarsa ga nauyi

yă miƙa kai ga aikin dole.

16 “Dan zai tanada adalci wa mutanensa

kamar ɗaya cikin kabilan Isra’ila.

17 Dan zai zama maciji a gefen hanya,

kububuwa a bakin hanya,

da take saran ɗiɗɗigen doki

domin mahayinsa yă fāɗi da baya.

18 “Ina zuba ido ga cetonka, ya Ubangiji.

19 “Masu fashi za su fāɗa wa Gad,

amma zai runtume su.

20 “Abincin Asher zai zama a wadace,

zai yi tanadin abinci iri-iri da suka dace don sarki.

21 “Naftali sakakkiyar barewa ce

da take haihuwar kyawawan ’ya’ya.

22 “Yusuf kuringa ce mai ba da amfani.

Kuringa mai ba da amfani kusa da rafi

wadda rassanta na hawan bango.

23 Da ɗaci rai mahara suka fāɗa masa;

suka harbe shi babu tausayi.

24 Amma bakansa yana nan daram

hannuwansa masu ƙarfi ba sa jijjiguwa

saboda hannun Maɗaukaki na Yaƙub,

saboda Makiyayi, Dutsen Isra’ila,

25 saboda Allah na mahaifinka, wanda ya taimake ka,

saboda Maɗaukaki, wanda yake albarkace ka

da albarkar sama da take bisa

albarkun zurfafa da suke ƙarƙashin ƙasa

albarkun mama da kuma mahaifa.

26 Albarkun mahaifi suna da girma fiye

da albarkun daɗaɗɗun duwatsu

fiye da yalwar madawwaman tuddai.

Bari dukan waɗannan su zauna a kan Yusuf,

a goshin ɗan sarki a cikin ’yan’uwansa.

27 “Benyamin kyarkeci ne mai kisa;

da safe yakan cinye abin da ya farauto

da yamma yakan raba ganima.”

28 Dukan waɗannan su ne kabilu goma sha biyu na Isra’ila, kuma abin da mahaifinsu ya faɗa musu ke nan sa’ad da ya albarkace su, yana ba kowane albarkar da ta dace da shi.

29 Sa’an nan ya ba su waɗannan umarnai ya ce, “Ina gab da a tara ni ga mutanena. Ku binne ni tare da kakannina a kogon da yake cikin filin Efron mutumin Hitti, 30 kogon da yake cikin filin Makfela, kusa da Mamre a Kan’ana, wanda Ibrahim ya saya tare da filin, yă zama makabarta daga Efron mutumin Hitti. 31 A can aka binne Ibrahim da matarsa Saratu, a can aka binne Ishaku da matarsa Rebeka, a can kuma na binne Liyatu. 32 Filin tare da kogon da yake ciki, an saya daga Hittiyawa.”

33 Sa’ad da Yaƙub ya gama ba da umarnan ga ’ya’yansa maza, sai ya ɗaga ƙafafunsa zuwa gado, ya ja numfashinsa na ƙarshe, aka kuwa tara shi ga mutanensa.