Ishaya Ya Annabta Halakar Taya

715 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Ishaya 23

1 Abin da Allah ya faɗa game da Taya.

Ku yi kuka mai zafi, ya jiragen ruwan Tarshish!

Gama an hallaka Taya

aka kuma bar su babu gida ko tasha.

Daga ƙasar Saifurus

magana ta zo musu.

2 Ku yi shiru, ku mutanen tsibiri

da ku ’yan kasuwan Sidon

waɗanda masu ciniki a teku suka azurta.

3 A manyan ruwaye

hatsin Shihor suka iso;

girbin Nilu ne kuɗin shiga na Taya

ta kuma zama kasuwar al’ummai.

4 Ki ji kunya, ya ke Sidon, da ke kuma, kagarar teku,

gama teku ya yi magana ya ce,

“Ban taɓa naƙuda ba balle in haifi ’ya’ya;

ban taɓa goyon ’ya’ya maza ba balle in reno ’ya’ya mata.”

5 Sa’ad da magana ta kai Masar,

za su razana da jin labari daga Taya.

6 Ku haye zuwa Tarshish;

ku yi kuka mai zafi, ku mutanen tsibiri.

7 Wannan ce birnin murnanku,

birnin nan na tun dā

wadda ƙafafunta suka kai ta

zama a ƙasashe masu nesa?

8 Wane ne ya ƙulla wannan a kan Taya

ita da take ba da rawanin sarauta,

wadda ’yan kasuwanta sarakuna ne,

wadda masu cinikinta sanannu ne a duniya?

9 Ubangiji Maɗaukaki ya ƙulla shi,

don yă kawo ƙarshen girman kan dukan darajarta

ya kuma ƙasƙantar da dukan waɗanda suke sanannu a duniya.

10 Ki nome ƙasarki har zuwa wajen Nilu,

Ya Diyar Tarshish,

gama ba ki da tashan jirgin ruwa kuma.

11 Ubangiji ya miƙa hannunsa a bisa teku

ya kuma sa mulkokinsa suka yi rawar jiki.

Ya ba da umarni game da Funisiya

cewa a hallaka kagararta.

12 Ya ce, “Ba za ki ƙara yin murna ba,

Ya ke Budurwa Diyar Sidon, yanzu da kike ragargajiya!

“Tashi, ki ƙetare zuwa Saifurus;

a can ɗin ma ba za ki huta ba.”

13 Dubi ƙasar Babiloniyawa,

wannan mutanen da yanzu ba su da wani amfani!

Assuriyawa sun mai da ita

wurin zaman halittun hamada;

sun gina hasumiyoyin kwanto,

suka ragargaza kagararta ƙaf

suka mai da ita kango.

14 Ku yi kuka mai zafi, ku jiragen ruwan Tarshish;

an rurrushe kagararku!

15 A wannan lokaci za a manta da Taya har shekaru saba’in, tsawon rayuwar sarki. Amma a ƙarshen waɗannan shekaru saba’in, zai zama wa Taya kamar yadda yake a waƙar karuwa cewa,

16 “Ɗauki garaya, ki ratsa birni,

Ya ke karuwar da aka manta da ita;

kaɗa garaya da kyau, ki rera waƙoƙi masu yawa,

saboda a tuna da ke.”

17 A ƙarshen shekaru saba’in, Ubangiji zai magance Taya. Za tă koma ga aikinta na karuwanci za tă kuma yi kasuwancinta da dukan mulkokin duniya. 18 Duk da haka za a keɓe ribarta da kuɗin shigarta wa Ubangiji; ba za a yi ajiyarsu ko a ɓoye su. Ribarta za tă tafi ga waɗanda suke yi wa Ubangiji sujada, don su sami yalwataccen abinci da tufafi masu kyau.

Ishaya Ya Annabta Mamayar Assuriyawa

Annabcin Ishaya game da mamayar Falasɗinu da sojojin Assuriya za su yi.

Ishaya 10:5–34

5 “Kaiton Assuriya, sandar fushina,

a hannun da kulkin fushina yake!

6 Na aike shi gāba da al’umma marar sanin Allah,

na tura shi gāba da mutanen da suka ba ni fushi,

don yă kwashe ganima yă kuma yi wason ganima,

yă tattake su kamar laka a tituna.

7 Amma ba abin da ya yi niyya ke nan ba,

ba abin da yake da shi a zuciya ba;

manufarsa shi ne yă hallaka,

yă kuma kawo ƙarshen al’ummai da yawa.

8 Ya ce, ‘Dukan shugabannin yaƙina ba sarakuna ba ne?’

9 ‘Kalno bai kasance kamar Karkemish ba?

Hamat bai zama kamar Arfad

Samariya kuma kamar Damaskus ba?

10 Yadda hannuna ya ƙwace mulkokin gumaka,

mulkokin da siffofinsu suka fi na Urushalima da Samariya,

11 ba zan yi da Urushalima da siffofinta

yadda na yi da Samariya da gumakanta ba?’ ”

12 Sa’ad da Ubangiji ya gama dukan aikinsa gāba da Dutsen Sihiyona da Urushalima, zai ce, “Zan hukunta sarkin Assuriya saboda fariya na gangancin zuciyarsa da kuma kallon reni na idanunsa. 13 Gama ya ce,

“ ‘Ta wurin ƙarfin hannuna ne na aikata wannan,

da kuma ta wurin hikimata, gama ina da fahimi.

Na kau da iyakokin ƙasashe,

na washe dukiyarsu;

a matsayina na mai iko, na mamaye sarakunansu.

14 Kamar yadda mutum yakan miƙa hannu cikin sheƙar tsuntsu

haka hannuna ya je ya washe dukiyar al’ummai;

kamar yadda mutane sukan tattara ƙwai,

haka na tattara dukan ƙasashe;

ba tsuntsun da ya kakkaɓe fikafiki,

ko yă buɗe baki don yă yi kuka.’ ”

15 Gatari ya taɓa fin wanda yake amfani da shi girma,

ko zarto yă yi wa wanda yake amfani da shi taƙama?

Sanda za tă girgiza mutumin da yake riƙe da ita,

ko kuwa kulki yă jijjiga mutumin da yake riƙe da katako!

16 Saboda haka Ubangiji Maɗaukaki,

zai aukar da cuta mai kisa a kan ƙosassu jarumawa;

a ƙarƙashin sansaninsa zai ƙuna wuta

kamar harshen wuta.

17 Hasken Isra’ila zai zo kamar wuta,

Mai Tsarkinsu zai zama kamar wuta;

a rana guda zai ƙone yă kuma cinye

ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiyarsa.

18 Darajar jejinsa da gonakinsa masu dausayi

za a hallaka su ɗungum,

kamar yadda ciwo yakan kashe mutum.

19 Sauran itatuwan jejinsa kuma za su ragu

ko ɗan ƙaramin yaro ma zai iya ƙidaya su.

20 A wannan rana raguwar Isra’ila,

waɗanda suka ragu na gidan Yaƙub,

ba za su ƙara dogara ga

wanda ya kusa hallaka su ba

amma za su dogara ga Ubangiji,

Mai Tsarkin nan na Isra’ila.

21 Raguwa za tă komo, raguwar Yaƙub

za su komo ga Maɗaukaki Allah.

22 Ko da yake mutanenka, ya Isra’ila, sun zama kamar yashin bakin teku,

raguwa ce kurum za tă komo.

A ƙaddara hallaka,

mai mamayewa da mai adalci.

23 Ubangiji Maɗaukaki, zai sa

hallakar da aka ƙaddara a kan dukan ƙasa ta faru.

24 Saboda haka, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce,

“Ya mutanena masu zama a Sihiyona,

kada ku ji tsoron Assuriyawa,

waɗanda suka dūke ku da sanda

suka kuma ɗaga kulki a kanku, kamar yadda Masar ta yi.

25 Ba da daɗewa ba fushina a kanku zai zo ga ƙarshe

hasalata kuma za tă koma ga hallakarsu.”

26 Ubangiji Maɗaukaki zai bulale su da tsumagiya,

kamar sa’ad da ya bugi Midiyan a dutsen Oreb;

zai kuma ɗaga sandarsa a bisa ruwaye,

yadda ya yi a Masar.

27 A wannan rana zai ɗauke nauyi daga kafaɗarku,

nauyinsu daga wuyanku;

za a karye karkiya

domin kun yi ƙiba ƙwarai.

28 Sun shiga Ayiyat;

sun bi ta Migron;

sun adana tanade-tanade a Mikmash.

29 Suka ƙetare ta hanya, suka kuma ce,

“Za mu kwana a Geba.”

Rama ta firgita;

Gibeya ta Shawulu ta gudu.

30 Ki yi ihu, ya Diyar Gallim!

Ki saurara, ya Layisha!

Kayya, Anatot abin tausayi!

31 Madmena tana gudu;

mutanen Gebim sun ɓuya.

32 A wannan rana za su dakata a Nob;

za su jijjiga ƙarfinsu

a dutsen Diyar Sihiyona,

a tudun Urushalima.

33 Duba, Ubangiji Maɗaukaki,

zai ragargaza rassa da iko mai girma.

Za a sassare itatuwa masu ganyaye,

za a yanke dogayen itatuwa har ƙasa.

34 Zai sassare itatuwan jeji da gatari har ƙasa;

Lebanon zai fāɗi a gaban Mai Iko.