Alƙawarin Allah da Abram

1912 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Farawa 15

1 Bayan wannan, maganar Ubangiji ta zo wa Abram cikin mafarki cewa,

“Kada ka ji tsoro, Abram.

Ni ne garkuwarka,

kuma ladanka zai zama mai girma.”

2 Amma Abram ya ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, mene ne za ka ba ni, ganin cewa ba na haihuwa, wanda kuma zai gāji gādon gidana shi ne Eliyezer mutumin Damaskus?” 3 Abram ya kuma ce, “Ga shi ba ka ba ni ɗa ba, don haka bawan da aka haifa a gidana ne zai zama magājina.”

4 Sa’an nan maganar Ubangiji ta zo gare shi cewa, “Wannan mutum ba zai zama magājinka ba, ɗa da yake zuwa daga jikinka ne zai zama magājinka.” 5 Sai Ubangiji ya fito da kai shi waje ya ce, “Ka dubi sammai ka kuma ƙirga taurari, in har za ka iya ƙirga su.” Sa’an nan ya ce masa, “Haka zuriyarka za tă zama.”

6 Abram ya gaskata, Ubangiji kuma ya lasafta shi adalci ga Abram.

7 Ubangiji ya kuma ce wa Abram, “Ni ne Ubangiji wanda ya fitar da kai daga Ur na Kaldiyawa, domin in ba ka wannan ƙasa ka mallake ta.”

8 Amma Abram ya ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, yaya zan san cewa zan mallake ta?”

9 Saboda haka Allah ya ce masa, “Kawo mini karsana, akuya, da kuma rago kowanne yă kasance shi shekara uku ne, da kurciya da kuma ɗan tattabara.”

10 Abram ya kawo waɗannan duka a gaban Allah, ya raba kowannensu a tsakiya, ya ajiye su gab da juna, amma bai tsaga tsuntsayen a tsaka ba. 11 Sai tsuntsaye masu cin nama suka sauko a kan gawawwakin, amma Abram ya kore su.

12 Yayinda rana tana fāɗuwa, sai Abram ya yi barci mai zurfi, sai wani duhu mai kauri mai kuma bantsoro ya rufe shi.

13 Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Abram, “Ka sani tabbatacce cewa shekaru ɗari huɗu, zuriyarka za tă zama baƙi a ƙasar da ba tasu ba, za a mai da su bayi, a kuma wulaƙanta su. 14 Amma zan hukunta al’ummar da suka yi bauta kamar bayi, daga baya kuma za su fita da mallaka mai yawa. 15 Amma kai za ka koma wurin kakanninka cikin salama a kuma binne ka da kyakkyawan tsufa. 16 A tsara ta huɗu zuriyarka za tă komo nan, saboda zunubin Amoriyawa bai riga ya cika ba.”

17 Sa’ad da rana ta fāɗi, aka kuwa yi duhu, sai wata tukunya mai hayaƙi, mai harshen wuta mai ci, ta bayyana, ta kuma wuce tsakanin abubuwan nan da aka tsaga. 18 A wannan rana, Ubangiji ya yi alkawari da Abram ya ce, “Ga zuriyarka na ba da wannan ƙasa, daga kogin Masar zuwa babban kogi, Yuferites ke nan, 19 ƙasar Keniyawa, Kenizziyawa, Kadmoniyawa, 20 Hittiyawa, Ferizziyawa, Refahiyawa, 21 Amoriyawa, Kan’aniyawa, Girgashiyawa da kuma Yebusiyawa.”

Haihuwar Ishmayel

Farawa 16

1 To, Saira, matar Abram, ba tă haifa masa ’ya’ya ba. Amma tana da wata baiwa mutuniyar Masar mai suna Hagar, 2 saboda haka sai ta ce wa Abram, “Ubangiji ya hana mini haihuwar ’ya’ya. Tafi ka kwana da baiwata; wataƙila in sami iyali ta wurinta.”

Abram kuwa ya yarda da abin da Saira ta faɗa. 3 Saboda haka bayan Abram ya yi zama a Kan’ana shekaru goma, Saira matarsa ta ɗauki Hagar baiwarta ta ba wa mijinta tă zama matarsa. 4 Abram kuwa ya kwana da Hagar, ta kuma yi ciki.

Sa’ad da Hagar ta gane tana da ciki, sai ta fara rena uwargijiyarta. 5 Sai Saira ta ce wa Abram, “Kai ne da alhakin wahalan nan da nake sha. Na sa baiwata a hannunka, yanzu da ta sani tana da ciki, sai ta fara rena ni. Bari Ubangiji yă shari’anta tsakanina da kai.”

6 Abram ya ce, “Baiwarki tana a hannunki? Ki yi da ita yadda kika ga ya fi kyau.” Sai Saira ta wulaƙanta Hagar; saboda haka ta gudu daga gare ta.

7 Mala’ikan Ubangiji ya sami Hagar kusa da maɓulɓula a jeji, ita ce maɓulɓular da take gefen hanya zuwa Shur. 8 Ya kuma ce mata, “Hagar, baiwar Saira, daga ina kika fito, kuma ina za ki?”

Ta amsa ta ce, “Ina gudu ne daga wurin uwargijiyata Saira.”

9 Sai mala’ikan Ubangiji ya ce mata, “Koma wurin uwargijiyarki Saira, ki yi mata biyayya.” 10 Mala’ikan ya ƙara da cewa, “Zan ƙara zuriyarki har su yi yawan da ba wanda zai iya lasafta su.”

11 Mala’ikan Ubangiji ya kuma ce mata,

“Ga shi kina da ciki

za ki kuwa haifi ɗa.

Za ki ba shi suna Ishmayel,

gama Ubangiji ya ga wahalarki.

12 Zai zama mutum mai halin jakin jeji.

Hannunsa zai yi gāba da kowa,

hannun kowa kuma zai yi gāba da shi.

Zai yi zama gāba

ga dukan ’yan’uwansa.”

13 Sai ta ba wa Ubangiji wanda ya yi magana da ita, wannan suna. “Kai Allah ne wanda yake ganina,” gama ta ce, “Yanzu na ga wanda yake ganina.” 14 Shi ya sa ake kira rijiyar Beyer-Lahai-Royi tana nan har yanzu, tsakanin Kadesh da Bered.

15 Haka fa Hagar ta haifa wa Abram ɗa, Abram kuwa ya ba da suna Ishmayel ga ɗan da ta haifa. 16 Abram yana da shekaru 86 sa’ad da Hagar ta haifa masa Ishmayel.