Sashe na 4: Sauran Gine-ginen Solomon da Ƙawarsa

Allah Ya Bayyana ga Solomon

Gina Gidan Dajin Lebanon. Allah ya bayyana ga Solomon.

1004 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

1 Sarakuna 7:1–12

1 Ya ɗauki Solomon shekaru goma sha uku kafin yă gama gina fadarsa. 2 Ya gina fadarsa mai suna Kurmin Lebanon, tsawonsa kamu ɗari, fāɗinsa kamu hamsin, tsayinsa kuma kamu talatin, a bisa jeri huɗu na ginshiƙan itacen al’ul, aka shimfiɗa katakan itacen al’ul a bisa ginshiƙan. 3 Aka yi rufin da al’ul bisa ginshiƙan da suke bisa ginshiƙai arba’in da biyar, goma sha biya a kowane jeri. 4 Aka kuma yi tagogi masu sandunan ƙarfe, jeri uku, kowace taga tana ɗaura da ’yar’uwarta, har jeri uku. 5 Dukan ƙofofin da madogaransu murabba’i ne, taga kuma tana ɗaura da ’yar’uwarta har jeri uku.

6 Ya yi babban zaure mai ginshiƙai, tsawonsa kamu hamsin, fāɗinsa kuwa kamu talatin. A gabansa kuwa akwai shirayi, kuma a gaban wannan shirayi akwai ginshiƙai da kuma rufin da yake a shimfiɗe.

7 Ya kuma gina shirayi ta sarauta, da ya kira Zauren Adalci, inda zai riƙa yin shari’a, ya kuma rufe dukan daɓensa da itacen al’ul daga ƙasa har sama. 8 A fadar da zai zauna kuwa, wadda aka gina a can baya, ya yi ta da irin fasali guda. Solomon ya kuma yi wata fada kamar wannan zaure domin ’yar Fir’auna, wadda ya auro.

9 Dukan waɗannan gine-gine, daga waje zuwa babban fili, da kuma daga tushen zuwa rufin, an yi su da duwatsun da aka yanka, aka kuma gyara da zarto a fuskokinsu na ciki da waje. 10 Aka kafa tushen da manyan duwatsu masu kyau, tsayin waɗansunsu ya kai kamu goma, waɗansu kuma kamu takwas. 11 A can bisa akwai duwatsu masu tsada da aka yayyanka bisa ga ma’auni, da kuma ginshiƙan al’ul. 12 An kewaye babban filin da katanga da jerin uku-uku na duwatsun da aka gyara, da kuma jeri guda na gyararren al’ul, kamar yadda aka yi na filin cikin haikalin Ubangiji da shirayinsa.

2 Tarihi 7:11–22

11 Sa’ad da Solomon ya gama haikalin Ubangiji da kuma fadan sarki ya kuma yi nasara a yin dukan abin da yake a zuciyarsa da zai yi a haikalin Ubangiji da kuma a fadarsa, 12 sai Ubangiji ya bayyana gare shi a daren ya ce,

“Na ji addu’arka na kuma zaɓi wannan wuri don kaina, a matsayin haikali don hadayu.

13 “Sa’ad da na kulle sammai don kada a yi ruwan sama ko na umarci fāri su cinye amfanin ƙasar ko kuwa na aika da annoba a cikin mutanena, 14 in mutanena, waɗanda ake kira da sunana, sun ƙasƙantar da kansu, suka kuma yi addu’a, suka nemi fuskata, suka kuma juye daga mugayen hanyoyinsu, zan ji daga sama in kuma gafarta zunubinsu in kuwa warkar da ƙasarsu. 15 Yanzu, idanuna za su buɗu, kunnuwata kuma za su saurara ga addu’o’in da aka miƙa a wannan wuri. 16 Na zaɓi na kuma tsarkake wannan haikali saboda Sunana yă kasance a can har abada. Idanuna da kuma zuciyata kullum za su kasance a can.

17 “Game da kai kuwa, in ka yi tafiya a gabana kamar yadda Dawuda mahaifinka ya yi, ka kuma yi dukan abin da na umarta, ka kiyaye ƙa’idodina da dokokina, 18 zan kafa kujerar sarautarka, yadda na alkawarta wa Dawuda mahaifinka sa’ad da na ce, ‘Ba za ka taɓa rasa wani mutumin da zai yi mulki a bisa Isra’ila ba.’

19 “Amma in ka juya daga gare ni ka yashe ƙa’idodi da umarnan da na ba ka, ka yi gaban kanka don ka bauta wa waɗansu alloli ka kuma yi musu sujada, 20 zan tumɓuke Isra’ila daga ƙasata, wadda na ba su, zan kuma ƙi wannan haikalin da na tsarkake domin Sunana. Zan mai da shi abin karin magana da abin ba’a cikin dukan mutane. 21 Ko da yake wannan haikali yanzu mai girma ne, dukan wanda ya wuce zai kaɗa kai yă ce, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi irin wannan abu ga wannan ƙasa da kuma ga wannan haikali?’ 22 Mutane za su amsa, ‘Domin sun yashe Ubangiji Allah na kakanninsu, wanda ya fitar da su daga Masar, suka rungumi waɗansu alloli, suna musu sujada, suna bauta musu, shi ya sa ya kawo dukan wannan masifa a kansu.’ ”

1 Sarakuna 9:1–9

1 Sa’ad da Solomon ya gama ginin haikalin Ubangiji da kuma fadan sarki, ya kuma yi dukan abin da yake so yă yi, 2 sai Ubangiji ya bayyana gare shi sau na biyu, kamar yadda ya bayyana masa a Gibeyon. 3 Ubangiji ya ce masa,

“Na ji addu’arka da kuma roƙon da ka yi a gabana; na tsarkake wannan haikali wanda ka gina, ta wurinsa Sunana zai kasance a can har abada. Idanuna da zuciyata kullum za su kasance a can.

4 “Kai kuwa, in ka yi tafiya a gabana da mutunci a zuci da kuma gaskiya, kamar yadda Dawuda mahaifinka ya yi, ka yi dukan abin da na umarta, ka kuma yi biyayya da ƙa’idodina da kuma dokokina, 5 zan kafa kujerar sarautarka a bisa Isra’ila har abada, kamar yadda na alkawarta wa Dawuda mahaifinka sa’ad da na ce, ‘Ba za ka taɓa rasa wani a kan kujerar sarautar Isra’ila ba.’

6 “Amma in kai, ko ’ya’yanka maza, suka juye daga gare ni, ba ku kuma kiyaye umarnai da ƙa’idodin da na ba ku ba, kuka yi gaba, kuka bauta wa waɗansu alloli, kuka kuma yi musu sujada, 7 sai in yanke mutanen Isra’ila daga ƙasar da na ba su, in kuma ƙi wannan haikalin da na tsarkake domin Sunana. Isra’ila kuwa za tă zama abin gori da abin dariya a cikin dukan mutane. 8 Wannan haikali zai zama tarin juji. Duk wanda ya wuce ta hanyan nan kuwa zai ji tausayi, yă kuma yi tsaki yana cewa, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi haka ga wannan ƙasa da kuma wannan haikali?’ 9 Mutane za su amsa su ce, ‘Saboda sun yashe Ubangiji Allahnsu, wanda ya fitar da su daga Masar, suka rungumi waɗansu alloli, suna yin musu sujada, suna bauta musu ne, ya sa Ubangiji ya kawo dukan masifan nan a kansu.’ ”

Yankunan da Solomon Ya Ci da Yaƙi da Sauran Ayyukansa 1001 kafin haihuwar Almasihu

1 Sarakuna 9:10–14

10 A ƙarshen shekaru ashirin da Solomon ya ɗauka yana gina haikalin Ubangiji da fadan sarki, 11 sai Sarki Solomon ya ba wa Hiram sarkin Taya garuruwa ashirin a yankin Galili, gama Hiram ya tanada masa da dukan katakai al’ul da na fir, da kuma zinariyar da ya bukaci domin aiki. 12 Amma sa’ad da Hiram ya zo daga Taya don yă ga garuruwan da Solomon ya ba shi, sai bai ji daɗi ba. 13 Sai ya ce, “Wanda irin garuruwa ke nan ka ba ni, ɗan’uwana?” Saboda haka ya kira su Ƙasar Kabul, sunan da suke da shi har wa yau. 14 Hiram kuwa ya aika wa sarki talenti 120 na zinariya.

2 Tarihi 8:1–11

1 A ƙarshen shekaru ashirin, a lokacin da Solomon ya gina haikalin Ubangiji da nasa fadan, 2 Solomon ya sāke gina ƙauyukan da Hiram ya ba shi, ya kuma zaunar da Isra’ilawa a cikinsu. 3 Sa’an nan Solomon ya tafi Hamat-Zoba ya ci ta da yaƙi. 4 Ya kuma gina Tadmor a hamada da kuma dukan biranen ajiyar da ya gina a Hamat. 5 Ya sāke gina Bet-Horon na Bisa da kuma Bet-Horon na Ƙasa a matsayin birane masu katanga, da bangaye da ƙofofi da kuma ƙyamare, 6 haka kuma Ba’alat da dukan biranen ajiyarsa, da kuma dukan birane domin keken yaƙinsa da dawakansa, duk abin da ya so yă gina a Urushalima, a Lebanon da kuma dukan yankin da ya yi mulki, ya gina shi.

7 Dukan mutanen da suka rage daga Hittiyawa, Amoriyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa (waɗannan mutane ba Isra’ilawa ba ne), 8 wato, zuriyarsu da suka ragu a ƙasar, wadda Isra’ilawa ba su hallaka ba, waɗannan ne Solomon ya mai da su bayinsa na aikin dole, kamar yadda yake har wa yau. 9 Amma Solomon bai mai da Isra’ilawa bayi don aikinsa ba; su ne mayaƙansa, shugabannin hafsoshinsa, da shugabannin keken yaƙinsa da kuma mahayan keken yaƙinsa. 10 Su ne kuma manyan ma’aikatan Sarki Solomon, manyan mutane ɗari biyu da hamsin masu lura da mutane.

11 Solomon ya kawo ’yar Fir’auna daga Birnin Dawuda zuwa fadan da ya gina mata, gama ya ce, “Matata ba za tă zauna a fadan Dawuda sarkin Isra’ila ba, domin wuraren da akwatin alkawarin Ubangiji ya shiga masu tsarki ne.”

1 Sarakuna 9:24

24 Bayan ’yar Fir’auna ta haura daga Birnin Dawuda zuwa fadan da Solomon ya gina mata, sai ya gina madogaran gini.