Annabcin Ezekiyel na Ƙarshe a Kan Masar

Annabcin ƙarshe a kan Masar.

572 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Ezekiyel 29:17–30:19

17 A shekara ta ashirin da bakwai, a wata na fari a rana ta farko, maganar Ubangiji ta zo mini cewa, 18 “Ɗan mutum, Nebukadnezzar sarkin Babilon ya sa sojojinsa su matsa wa Taya; kowane kai ya koɗe, kowace kafaɗa kuma ta goge. Duk da haka shi da sojojinsa ba su sami wani lada daga matsin da suka yi a kan Taya ba. 19 Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan ba da Masar ga Nebukadnezzar sarkin Babilon, zai washe dukiyarta. Zai kwashe ya washe ƙasar ganima a matsayin abin biyan sojojinsa. 20 Saboda haka na ba shi Masar a matsayin lada don ƙoƙarinsa domin shi da sojojinsa sun yi wannan domina ne, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

21 “A wannan rana zan sa ƙaho ya tsiro wa gidan Isra’ila, zan kuma buɗe bakinka a cikinsu. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.”

30:1 Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, 2 “Ɗan mutum, ka yi annabci ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,

“ ‘Yi kuka kana cewa,

“Kaito saboda wannan rana!”

3 Gama ranar ta yi kusa,

ranar Ubangiji ta gabato,

ranar gizagizai,

lokacin hallaka wa al’ummai.

4 Takobi zai zo a kan Masar,

azaba za tă zo a kan Kush.

Sa’ad da kisassu za su fāɗi a Masar,

za a kwashe dukiyarta a tafi

a rushe harsashinta.

5 Kush da Fut, Lidiya da dukan Arabiya, Libiya da kuma mutanen ƙasar alkawari za su mutu ta wurin takobi tare da Masar.

6 “ ‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa,

“ ‘Waɗanda suke goyon bayan Masar za su fāɗi

ƙarfinta da take fariya da shi zai ƙare.

Daga Migdol zuwa Aswan

za su mutu ta wurin takobi a cikinta,

in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

7 Za su zama kango

a cikin ƙasashen da suke kango,

biranensu kuwa za su zama kufai

a cikin biranen da suka lalace.

8 Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji,

sa’ad da suka ga na sa wuta wa Masar

aka kuma ragargaza masu taimakonta.

9 “ ‘A wannan rana manzanni za su fito daga wurina a jiragen ruwa don su tsorata Kush daga sake jikinta. Azaba za tă kama su a ranar hallakar Masar, gama tabbatacce za tă zo.

10 “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,

“ ‘Zan kawo ƙarshen mutanen Masar

ta hannun Nebukadnezzar sarkin Babilon.

11 Shi da sojojinsa, mafi bantsoro cikin al’ummai,

za a kawo don su hallaka ƙasar.

Za su zāre takuba a kan Masar

su kuma cika ƙasar da kisassu.

12 Zan kafe rafuffukan Nilu

in sayar da ƙasar ga mugayen mutane;

ta hannun baƙi

zan sa ƙasar ta lalace da kome da yake cikinta.

Ni Ubangiji na faɗa.

13 “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,

“ ‘Zan hallaka gumaka

in kuma kawo ƙarshen siffofi a Memfis.

Ba za a ƙara samun yerima a ƙasar Masar ba,

zan kuma baza tsoro a duk fāɗin ƙasar.

14 Zan lalace Masar ta Bisa

in ƙuna wuta wa Zowan

in zartar da hukunci a kan Tebes.

15 Zan kwarara hasalata a kan Felusiyum,

kagarar Masar,

in kuma datse mutanen Tebes.

16 Zan ƙuna wuta wa Masar;

Felusiyum za tă sha azaba mai zafi.

Za a tayar wa Tebes da hankali;

Memfis za tă riƙa kasance cikin ɓacin rai.

17 Samarin Heliyofolis da Bubastis

za su mutu ta wurin takobi,

biranen kansu za su tafi bauta.

18 Duhu ne zai zama rana a Tafanes

sa’ad da na karye ikon Masar;

a can ƙarfin da take fariya zai ƙare.

Za a rufe ta da gizagizai

ƙauyukanta kuma za su tafi bauta.

19 Ta haka zan zartar da hukunci a kan Masar,

za su kuwa san cewa ni ne Ubangiji.’ ”