Ezekiyel Ya Yi Annabci a Kan Fir’auna da Masar
Annabci a kan Masar.
589 kafin haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
1 A shekara ta goma, a wata na goma, a rana ta goma sha biyu, maganar Ubangiji ta zo mini cewa, 2 “Ɗan mutum, ka fuskanci Fir’auna sarkin Masar ka kuma yi annabci gāba da shi da dukan Masar. 3 Yi masa magana ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
“ ‘Ina gāba da kai, Fir’auna sarkin Masar,
kai babban mugun dodon ruwa kwance cikin rafuffukanka.
Ka ce, “Nilu nawa ne;
na yi shi wa kaina.”
4 Amma zan sa ƙugiyoyi a muƙamuƙanka
in sa kifin rafuffukanka su manne wa kamɓorinka.
Zan jawo ka daga cikin tsakiyar rafuffukanka,
da dukan kifayen rafuffukanka, waɗanda suka manne a ƙamborinka,
5 Zan bar ka a cikin hamada,
kai da dukan kifin rafuffukanka.
Za ka fāɗi a fili
ba kuwa za a tattara ka ko a kwashe ba.
Zan ba da kai kamar abinci
ga namun jeji na duniya da tsuntsayen sararin sama.
6 Ta haka dukan waɗanda suke zama a Masar za su san cewa ni ne Ubangiji.
“ ‘Ka zama sandan iwa domin gidan Isra’ila. 7 Sa’ad da suka kama ka da hannuwansu, ka tsattsage, ka kuma buɗu a kafaɗunsu; sa’ad da suka jingina a kanka, sai ka karye, bayansu kuwa ya firgita.
8 “ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan kawo takobi a kanka in kashe mutane da dabbobi. 9 Masar za tă zama kufai. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.
“ ‘Domin ka ce, “Nilu nawa ne; ni na yi shi,” 10 saboda haka ina gāba da kai da rafuffukanka, zan kuma maishe ƙasar Masar ta lalace ta kuma zama kango daga Migdol zuwa Aswan, har iyakar Kush. 11 Ba ƙafar mutum ko ta dabbar da za tă ratsa ta; ba wanda zai zauna a can har shekaru arba’in. 12 Zan mai da ƙasar Masar kufai a cikin ƙasashen da aka ragargaza, biranenta kuma za su zama kango har shekaru arba’in a cikin biranen da aka lalace. Zan watsar da Masarawa a cikin al’ummai in warwatsa su cikin ƙasashe.
13 “ ‘Duk da haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a ƙarshen shekaru arba’in ɗin zan tattara Masarawa daga al’ummai inda aka warwatsa su. 14 Zan komo da su daga zaman bauta in mai da su zuwa Masar ta Bisa, ƙasarsu ta ainihi. A can za su zama masarauta marar ƙarfi. 15 Za tă zama masarauta mafi rarrauna cikin masarautai, ba kuwa za tă ƙara ɗaga kanta a kan sauran al’ummai ba. Zan sa tă zama marar ƙarfi ƙwarai, har da ba za tă ƙara yin mulkin a kan al’ummai ba. 16 Masar ba za tă ƙara zama abin dogara ga mutanen Isra’ila ba amma za tă zama abin tunin zunubinsu na juyawa gare ta don taimako. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”
Ezekiyel: Masar Za Ta Faɗi Kamar Assuriya 588 kafin haihuwar Almasihu
Annabci a kan Masar.
20 A shekara ta goma sha ɗaya, a wata na fari a rana ta goma sha bakwai, maganar Ubangiji ta zo mini cewa, 21 “Ɗan mutum, na karye hannun Fir’auna sarkin Masar. Ba a daure shi don warkarwa ba ko a sa tsinke saboda kada yă zama da ƙarfi har ya riƙe takobi. 22 Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da Fir’auna sarkin Masar. Zan karye hannuwansa biyu, hannun da yake da kyau da kuma wanda an riga an karya, in kuma sa takobi ya fāɗi daga hannunsa. 23 Zan watsar da Masarawa a cikin al’ummai in warwatsa su cikin ƙasashe. 24 Zan ƙarfafa hannuwan sarkin Babilon in kuma sa takobina a hannunsa, amma zan karya hannuwan Fir’auna, zai kuwa yi nishi a gabansa kamar mutumin da aka yi wa raunin mutuwa. 25 Zan ƙarfafa hannuwan sarkin Babilon, amma hannuwan Fir’auna za su shanye. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na sa takobi a hannun sarkin Babilon na kuma miƙa shi a kan Masar. 26 Zan watsar da Masarawa a cikin al’ummai in warwatsa su cikin ƙasashe. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.”
31:1 A shekara ta goma sha ɗaya, a wata na uku a rana ta farko, maganar Ubangiji ta zo mini cewa, 2 “Ɗan mutum, faɗa wa Fir’auna sarkin Masar da jama’arsa cewa,
“ ‘Da wa za a kwatanta girmanka?
3 Ka dubi Assuriya, ta taɓa zama kamar al’ul a Lebanon
da rassa masu kyau suna inuwartar da kurmi;
ya yi tsayi ainun
kansa ya kai cikin gizagizai.
4 Ruwa ya sa ya yi girma,
zurfafan maɓulɓulai sun sa ya yi tsayi;
rafuffuka suna gudu
kewaye da tushensa
yana aika da rafuffukansa
zuwa dukan itatuwan kurmi.
5 Saboda haka ya yi tsayi
fiye da sauran itatuwan kurmi;
rassansa suka ƙaru
suka yi tsayi,
suka bazu saboda yalwar ruwaye.
6 Dukan tsuntsayen sararin sama
suka yi sheƙa a rassansa,
dukan namun jeji
suka haihu a ƙarƙashin rassansa;
dukan al’ummai
suka zauna a inuwarsa.
7 Yana da girma a kyau,
da dogayen rassansa da ya baza,
gama saiwoyinsa sun nutse can ƙasa
har cikin yalwar ruwaye.
8 Al’ul a cikin lambun Allah
ba su kai shi ba,
balle itatuwan kasharina
su kai rassansa,
ko itatuwan durumi
su kai rassansa,
ko itace a lambun Allah
ya kai kyansa.
9 Na sa ya yi kyau
da yalwar rassa,
abin ƙyashi na dukan itatuwan Eden
a lambun Allah.
10 “ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa domin ya yi tsayi, kansa kuma ya kai cikin gizagizai, kuma domin ya yi fariya saboda tsayinsa, 11 na miƙa shi ga mai mulkin al’ummai, don yă sāka masa gwargwadon muguntarsa. Na jefar da shi a gefe, 12 kuma baƙi mafi mugunta na al’ummai suka sare shi suka bar shi. Rassansa sun fāɗi a kan duwatsun da suke cikin dukan kwaruruka; rassansa kuma sun kakkarye, sun fāɗi a cikin dukan magudanan ruwa na ƙasa. Dukan al’umman duniya suka fito daga ƙarƙashin inuwarsa suka bar shi. 13 Dukan tsuntsaye sararin sama suka zauna a itacen da ya fāɗi, dukan namun jeji kuma suna cikin rassansa. 14 Saboda haka ba wani daga cikin itatuwan da suke kusa da ruwan da zai taɓa yin fariyar tsawonsa, har kawunansu su kai cikin gizagizai. Ba wani daga cikin itatuwan da ya sha ruwa sosai da zai taɓa yi wannan tsayi; duk an bashe su ga mutuwa, zuwa can ƙasa, a cikin matattu, tare da waɗanda suka gangara zuwa rami.
15 “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a ranar da aka yi ƙasa da shi zuwa kabari na rufe zurfafa maɓulɓulai da makoki dominsa; na janye rafuffukansa, aka kuma hana yalwan ruwansa. Saboda shi na rufe Lebanon da baƙin ciki, dukan itatuwan kurmi suka bushe. 16 Na sa al’ummai suka yi rawar jiki da jin ƙarar fāɗuwarsa sa’ad da na yi ƙasa da shi zuwa kabari tare da waɗanda suka gangara rami. Sai dukan itatuwan Eden, zaɓaɓɓu da kuma mafi kyau na Lebanon, dukan itatuwan da aka yi musu banruwa, sun ta’azantu a ƙarƙashin ƙasa. 17 Waɗanda suka zauna a inuwarsa, dukan masu tarayyarsa a cikin al’ummai, su ma sun gangara zuwa kabari tare da shi, sun haɗu da waɗanda aka kashe da takobi.
18 “ ‘Da wa cikin itatuwan Eden za a kwatanta da kai cikin girma da daraja? Duk da haka kai ma, za a yi ƙasa da kai tare da itatuwan Eden zuwa ƙarƙashin ƙasa; za ka kwanta a cikin marasa kaciya, tare da waɗanda aka kashe da takobi.
“ ‘Fir’auna ke nan da dukan jama’arsa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”