Elihu Ya Ce Wahala Tana Fitowa Daga Allah

Elihu, wanda ya yi shiru har zuwa yanzu, ya shiga muhawarar. Ya nuna cewa Allah yana aika wahala domin dalilai na hikima, ko da yake ba za mu iya gano su ba, kuma aikin mutum shi ne ya miƙa wuya.

2130 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Ayuba 32–33

1 Sai mutanen nan uku suka daina amsa wa Ayuba, domin a ganinsa shi mai adalci ne. 2 Amma Elihu ɗan Barakel mutumin Buz na iyalin Ram, ya ji haushi da Ayuba don yă nuna shi ne mai gaskiya ba Allah ba. 3 Ya kuma ji haushin abokan nan guda uku, don sun kāsa amsa wa Ayuba ko da yake sun nuna Ayuba ne yake da laifi. 4 Elihu ya jira sai a wannan lokaci ne ya yi magana da Ayuba, don shi ne yaro a cikinsu duka. 5 Amma sa’ad da Elihu ya ga mutanen nan uku ba su da abin cewa, sai ya fusata.

6 Sai Elihu ɗan Barakel mutumin Buz ya ce,

“Ni ƙarami ne a shekaru,

ku kuma kun girme ni;

shi ya sa na ji tsoro

na kāsa gaya muku abin da na sani.

7 Na ɗauka ya kamata ‘shekaru su yi magana;

ya kamata yawan shekaru su koyar da hikima.’

8 Amma ruhun da yake cikin mutum,

numfashin Maɗaukaki shi ne yake ba shi ganewa.

9 Ba tsofaffi ne kaɗai suke da hikima ba,

ba masu yawan shekaru ne suke gane abin da yake daidai ba.

10 “Saboda haka nake ce muku, ku saurare ni;

ni ma zan gaya muku abin da na sani.

11 Na jira sa’ad da kuke magana,

na ji muhawwararku

lokacin da kuke neman abin da za ku faɗa,

12 na saurare ku da kyau.

Amma ba waninku da ya nuna Ayuba yana da laifi;

ba ko ɗayanku da ya amsa muhawwararsa.

13 Kada ku ce, ‘Mun sami hikima;

Allah ne kaɗai yake da ikon yin nasara da shi ba mutum ba.’

14 Amma ba da ni Ayuba ya yi gardama ba

kuma ba zan amsa masa da irin amsarku ba.

15 “Mamaki ya kama su kuma ba su da abin cewa;

kalmomi sun kāsa musu.

16 Dole ne in jira yanzu da suka yi shiru,

yanzu da suke tsaye a wurin ba su da amsa.

17 Ni ma zan faɗi nawa;

ni ma zan faɗi abin da na sani.

18 Gama ina cike da magana,

kuma ruhun da yake cikina yana iza ni;

19 a ciki ina kamar ruwan inabi wanda aka rufe a cikin kwalaba,

kamar sabuwar salkar ruwan inabi mai shirin fashewa.

20 Dole in yi magana in sami lafiya;

dole in buɗe baki in ba da amsa.

21 Ba zan nuna wa wani sonkai ba,

ko kuma in yi wa wani daɗin baki ba;

22 gama da a ce na iya daɗin baki,

da wanda ya yi ni ya ɗauke ni daga nan tuntuni.

33:1 “Amma yanzu, Ayuba, ka saurari abin da zan ce;

ka sa hankali ga kowane abin da zan faɗa.

2 Zan yi magana;

kalmomina suna dab da fitowa daga bakina.

3 Abin da zan faɗa gaskiya ne daga cikin zuciyata;

bakina zai faɗi gaskiyar abin da na sani.

4 Ruhun Allah ne ya yi ni;

numfashin Maɗaukaki ya ba ni rai.

5 Ka amsa mini in za ka iya;

ka yi shirin fuskanta ta.

6 Ni kamar ka nake a gaban Allah;

ni ma daga ƙasa aka yi ni.

7 Kada ka ji tsorona,

ba abin da zai fi ƙarfinka.

8 “Amma ka faɗa na ji,

na ji daidai abin da ka faɗa,

9 ‘ni mai tsarki ne marar zunubi;

ina da tsabta kuma ba ni da laifi.

10 Duk da haka Allah ya same ni da laifi;

ya ɗauke ni maƙiyinsa,

11 ya daure ƙafafuna da sarƙa;

yana tsaron duk inda na bi.’

12 “Amma na gaya maka, a nan ba ka yi daidai ba,

gama Allah ya fi mutum girma.

13 Don me ka yi masa gunaguni

cewa ba ya amsa tambayoyin mutum?

14 Gama Allah yana magana,

yanzu ga wannan hanya, yanzu kuma ga wata hanya

ko da yake ba lalle mutum yă lura ba.

15 A cikin mafarki, cikin wahayi da dare,

sa’ad da barci mai zurfi ya fāɗo a kan mutane

lokacin da suke cikin barci kan gadajensu,

16 mai yiwuwa yă yi musu magana a cikin kunnuwansu

yă razana su da gargaɗinsa,

17 don a juyar da su daga abin da yake yi da ba daidai ba

a kuma hana su daga girman kai,

18 don a kāre su daga fāɗuwa cikin rami,

a kāre su daga hallaka ta wurin takobi.

19 “Ko kuma mutum yă sha horo

ta wurin kwanciya da ciwo da rashin jin daɗi cikin ƙasusuwansa,

20 yadda zai ji ƙyamar abinci,

har yă ƙi son abinci mafi daɗi.

21 Naman jikinsa ya lalace ba wani abu mai kyau a ciki

kuma ƙasusuwansa da suke a rufe da tsoka yanzu duk sun fito.

22 Ransa yana matsawa kusa da rami,

ransa kuma kusa da ’yan aikan mutuwa.

23 Duk da haka, in akwai mala’ika a gefensa kamar matsakanci,

ɗaya daga cikin dubu,

da zai gaya wa mutum abin da yake daidai gare shi,

24 yă yi masa alheri yă ce,

‘Kada ka bari yă fāɗa cikin rami,

na samu fansa dominsa.’

25 Sa’an nan fatar jikinsa za tă zama sabuwa kamar ta jariri;

za tă zama kamar lokacin da yake matashi.

26 Ya yi addu’a ga Allah ya kuwa samu alheri a wurinsa,

yana ganin fuskar Allah yana kuma yin sowa don murna;

Allah ya mayar da shi ya zama mai adalci.

27 Sa’an nan sai ya zo wurin, wurin mutane ya ce,

‘Na yi zunubi, na kauce wa abin da yake daidai,

amma ban samu abin da ya kamata in samu ba.

28 Ya fanshi raina daga fāɗawa cikin rami,

kuma zan rayu in ji daɗin hasken.’

29 “Allah ya yi wa mutum duk waɗannan,

sau biyu, har ma sau uku.

30 Ya juyo da ransa daga fāɗawa cikin rami,

don hasken rai ya haskaka a kansa.

31 “Ka sa hankali da kyau, Ayuba, ka saurare ni;

ka yi shiru zan yi magana.

32 In kana da abin da za ka ce, ka amsa mini;

yi magana, domin ina so in ’yantar da kai.

33 Amma in ba haka ba, sai ka saurare ni;

yi shiru, zan kuma koya maka hikima.”