Debora Annabiya Ta Yi Alƙalanci a Isra’ila

An tilasta wa Isra’ilawa na arewa su bauta wa Kan’aniyawa, kuma Debora annabiya ta zama alƙali.

1305 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Mahukunta 4

1 Bayan rasuwar Ehud, Isra’ilawa suka sāke aikata mugayen ayyuka a gaban Ubangiji. 2 Saboda haka Ubangiji ya sayar da su ga Yabin sarkin Kan’ana wanda yake mulki a Hazor. Shugaban mayaƙansa shi ne Sisera, wanda yake zaune a Haroshet Haggoyim. 3 Domin Yabin sarkin Kan’ana yana da kekunan yaƙin ƙarfe ɗari tara, ya ji wa Isra’ilawa ƙwarai har shekara ashirin, sai suka yi kuka ga Ubangiji, don taimako.

4 A lokacin Debora annabiya, matar Laffidot ce take bi da Isra’ila. 5 Takan yi zaman shari’a a ƙarƙashin Dabinon Debora tsakanin Rama da Betel, a ƙasar tudu ta Efraim, Isra’ilawa kuwa sukan zo wurinta don tă yi musu shari’a. 6 Sai ta aika a kira mata Barak ɗan Abinowam daga Kedesh a Naftali, ta ce masa, “Ubangiji, Allah na Isra’ila ya umarce ka, ‘Je ka, ka ɗauki mutane Naftali da na Zebulun dubu goma tare da kai, ka yi jagoransu zuwa Dutse Tabor. 7 Zan jawo Sisera, shugaban mayaƙan Yabin, da keken yaƙinsa da mayaƙansa zuwa Kogin Kishon in ba da su a hannunku.’ ”

8 Barak ya ce, “In kika tafi tare da ni, zan tafi; amma in ba ki zo tare da ni ba, ba zan tafi ba.”

9 Debora ta ce, “To, shi ke nan, zan tafi tare da kai. Amma saboda yadda ka ɗauki wannan batun, darajar ba za tă zama taka ba, gama Ubangiji zai ba da Sisera a hannun mace.” Saboda haka Debora ta tafi tare da Barak zuwa Kedesh, 10 a can Barak ya kira Zebulun da Naftali. Mutum dubu goma suka kuma bi shi, Debora kuma tana tare da shi.

11 To, Heber Bakene ya riga ya bar Keniyawa, zuriyar Hobab, ɗan’uwan matar Musa, ya kafa tentinsa wajen babban itace a Za’anannim kusa da Kedesh.

12 Sa’ad da aka gaya wa Sisera cewa Barak ɗan Abinowam ya haura zuwa dutsen Tabor, 13 sai Sisera ya tattara keken yaƙinsa na ƙarfe ɗari tara wuri ɗaya da dukan mutanen da suke tare da shi daga Haroshet Haggoyim zuwa Kogin Kishon.

14 Sa’an nan Debora ta ce wa Barak, “Je ka! Wannan ita ce ranar da Ubangiji ya ba da Sisera a hannunka. Ba Ubangiji ya riga ya sha gabanka?” Saboda haka Barak ya gangara zuwa Dutsen Tabor, da mutum dubu goma biye da shi. 15 Da matsowar Barak, Ubangiji ya murƙushe Sisera da dukan sarakunansa da mayaƙansa da takobi, Sisera kuwa ya gudu da ƙafa ya bar keken yaƙinsa. 16 Amma Barak ya bi keken yaƙin da mayaƙan har Haroshet Haggoyim. Aka karkashe dukan mayaƙan Sisera ba ko ɗayan da ya tsira.

17 Amma Sisera, ya tsere da ƙafa zuwa tentin Yayel, matar Heber Bakene, domin suna da abokantaka da Yabin sarkin Hazor da kuma kabilar Heber Bakene.

18 Yayel ta fito ta taryi Sisera ta ce masa, “Ranka yă daɗe, ka shigo, ka shigo ciki. Kada ka ji tsoro.” Saboda haka ya shiga cikin tentinta, sai ta rufe shi da bargo.

19 Sai ya ce, “Ina roƙonki, ki ba ni ruwa in sha, ina jin ƙishirwa.” Sai ta buɗe salkar madara, ta ba shi ya sha, sai ta kuma rufe shi.

20 Ya ce mata, “Ki tsaya a ƙofar tenti, in wani ya zo ya tambaye ki, ‘Akwai wani a nan?’ Ki ce masa ‘a’a.’ ”

21 Amma Yayel, matar Heber, ta ɗauki turken tenti da guduma ta tafi wurinsa da sauri sa’ad da yake barci saboda gajiya. Ta kafa masa turken a gindin kunnensa ta haɗa shi da ƙasa, har ya mutu.

22 Sai ga Barak mai bin sawun Sisera, Yayel kuwa ta fito don marabtarsa, ta ce, “Shigo, zan nuna maka mutumin da kake nema.” Saboda haka ya shiga ciki tare da ita, sai ga Sisera kwance da turken a gindin kunnensa, matacce.

23 A ranar Allah ya yi kaca-kaca da Yabin, sarkin Kan’ana a gaban Isra’ila. 24 Isra’ilawa kuwa suka ƙara ƙarfi gāba da Yabin, sarkin Kan’aniyawa, har suka hallaka shi.

Waƙar Debora da Barak 1285 kafin haihuwar Almasihu

Mahukunta 5

1 A wannan rana ce Debora da Barak ɗan Abinowam suka rera wannan waƙa.

2 “Sa’ad da ’ya’yan sarki a Isra’ila suka yi jagora,

sa’ad da mutane suka niyya su ba da kansu,

suna yabon Ubangiji!

3 “Ya sarakuna, ku ji! Ku saurara, ku masu mulki!

Zan yi waƙa ga Ubangiji, zan yi waƙa;

zan yi kaɗe-kaɗe ga Ubangiji, Allah na Isra’ila.

4 “Ya Ubangiji, sa’ad da ka bar Seyir,

sa’ad da ka yi tafiya daga ƙasar Edom,

ƙasa ta girgiza, sammai suka zubo,

gizagizai sun zubo da ruwa.

5 Duwatsu suka girgizu a gaban Ubangiji, Wannan na Sinai,

a gaban Ubangiji, Allah na Isra’ila.

6 “A zamanin Shamgar ɗan Anat,

a zamanin Yayel, an yashe dukan hanyoyi;

matafiye suka bi hanyoyin da suka yi kona-kona.

7 Rayuwar ƙauye a Isra’ila ta daina,

ta daina sai da ni, Debora, na taso,

na taso mahaifiya a Isra’ila.

8 Sa’ad da suka zaɓi sababbin alloli,

sai ga yaƙi a ƙofofin birnin,

ba a kuwa ga garkuwa ko māshi

a cikin mutum dubu arba’in a Isra’ila ba.

9 Zuciyata tana tare da ’ya’yan sarakunan Isra’ila,

tare da masu niyyar ba da kansu da yardan rai cikin mutane.

Yabo ya tabbata ga Ubangiji!

10 “Ku da kuke hawan fararen jakuna,

kuna zama a sirdin barguna,

da ku da kuke tafiya a kan hanya,

ku kula 11 da muryoyin mawaƙa a wuraren ruwaye.

Suna faɗi ayyukan adalcin Ubangiji,

ayyukan adalcin mayaƙansa a Isra’ila.

“Sa’an nan mutanen Ubangiji

suka gangara zuwa ƙofofin birni.

12 ‘Ki farka, ki farka, Debora!

Ki farka, ki farka, ki tā da waƙa!

Ka farka, ya Barak!

Ka ta sa kamammunka gaba, ya ɗan Abinowam.’

13 “Sa’an nan waɗanda aka bari

suka sauko zuwa wajen shugabanni;

mutane na Ubangiji

suka zo wurina tare da masu ƙarfi.

14 Waɗansu suka zo daga Efraim, waɗanda ainihinsu daga Amalek ne;

Benyamin yana tare da mutanen da suka bi ka.

Daga Makir, shugabannin sojoji suka gangaro,

daga Zebulun waɗanda suke riƙe da sandan komanda suka fito.

15 ’Ya’yan sarautar Issakar suna tare da Debora;

I, Issakar yana tare da Barak,

yana binsa a guje zuwa kwari.

A yankunan Ruben

aka kuma bincike zuciya sosai.

16 Don me kuka tsaya a wutar sansani

don ku ji makiyaya suna kiran garkuna?

A yankunan Ruben

aka yi bincike zuciya sosai.

17 Gileyad ya tsaya gaban Urdun.

Kai kuma Dan, don me ka ka yi ta zama a wajen jiragen ruwa?

Asher ya ci gaba da kasance a bakin teku

ya kasance a wuraren zamansa.

18 Mutanen Zebulun sun kasai da rayukansu;

haka ma Naftali a bakin dāgā.

19 “Sarakuna suka zo, suka yi yaƙi;

sarakunan Kan’ana sun yi yaƙi

a Ta’anak a gefen ruwan Megiddo,

amma ba su ɗauki azurfa, ko ganima ba.

20 Daga sama taurari suka yi faɗa,

daga bakin tekuna suka yi yaƙi da Sisera.

21 Kogin Kishon ya kwashe su,

tsohon kogi, kogin Kishon.

Ci gaba raina; ka ƙarfafa!

22 Sa’an nan kofatan dawakai suka ƙwaƙula,

suna sukuwa, haka dawakansa masu ƙarfi suke tafiya.

23 Mala’ikan Ubangiji ya ce, ‘Ka la’anci Meroz.’

‘Ka la’anci mutanensa sosai,

domin ba su kawo wa Ubangiji taimako ba,

su kawo wa Ubangiji taimako a kan masu ƙarfi ba.’

24 “Mafi albarka a ciki mata ta zama Yayel

matar Heber Bakene,

mafi albarka na mata masu zama a alfarma.

25 Ya nemi ruwa, ta kuwa ta ba shi madara;

a ƙwaryar da ta dace da sarakuna ta kawo masa kindirmo.

26 Hannunta ya ɗauki turken tenti,

da hannunta na dama ta ɗauko guduma.

Ta bugi Sisera, ta ragargaza kansa,

ta ragargaza ta huda kunnensa.

27 A ƙafafunta ya fāɗi,

ya fāɗi; a can ya kwanta.

A ƙafafunta ya fāɗi, ya fāɗi;

a can ya fāɗi, matacce.

28 “Ta taga mahaifiyar Sisera ta leƙa;

a bayan madogarar ƙofa ta yi ta ihu,

‘Me ya sa keken yaƙinsa ta daɗe ba tă dawo ba?

Me ya sa dawakan keken yaƙinsa ba su dawo da wuri ba?’

29 Mafi hikima cikin ’yan matanta suka amsa mata,

tabbatacce, ta ci gaba ta ce wa kanta,

30 ‘Ba nema suke su raba ganima ba,

yarinya guda ko biyu wa kowane mutum,

riguna masu launi a matsayin ganima don Sisera,

riguna masu ado,

riguna masu ado sosai don wuyata,

dukan wannan a matsayin ganima?’

31 “Ta haka bari dukan abokan gābanka su hallaka, ya Ubangiji!

Amma bari waɗanda suke ƙaunarka su zama kamar rana

sa’ad da ta fito da ƙarfinta.”

Sa’an nan ƙasar ta sami zaman lafiya shekara arba’in.