Alherin Dawuda ga Gidan Shawulu (continued)
Alherin Dawuda ga gidan Shawulu. Yaƙi da Ammonawa.
1040 kafin haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda.
1 Ya Ubangiji, sarki yana farin ciki cikin ƙarfinka.
Yana farin cikinsa ƙwarai cikin nasarorin da ka ba shi!
2 Ka biya masa bukatar zuciyarsa
ba ka kuwa hana masa roƙon da ya yi da leɓunansa ba. Sela
3 Ka marabce shi da yalwar albarka
ka kuma sa masa rawanin zallan zinariya a kansa.
4 Ya nemi ka ba shi rai, ka kuwa ba shi,
tsawo kwanaki, har abada abadin
5 Ta wurin nasarorin da ka ba shi, ɗaukakarsa mai girma ce;
ka mayar masa ɗaukaka da kuma suna.
6 Tabbatacce ka ba shi madawwamiyar albarka
ka kuma sa shi murna da farin cikin kasancewarka.
7 Gama sarki ya dogara gare ka Ubangiji
ta wurin ƙauna marar ƙarewa ta Mafi Ɗaukaka
ba zai jijjigu ba.
8 Hannunka zai kakkama dukan abokan gābanka;
hannunka na dama zai kakkama masu ƙinka.
9 A lokacin bayyanarka
za ka sa su zama kamar wutar matoya.
Cikin fushinsa Ubangiji zai haɗiye su,
kuma wutarsa za tă cinye su.
10 Za ka hallaka ’ya’yansu daga duniya,
zuriyarsu kuma daga ’yan adam.
11 Ko da yake suna shirya maka mugunta
suna kuma ƙirƙiro mugayen dabaru, ba za su yi nasara ba;
12 gama za ka sa su juye bayansu
sa’ad da ka auna su da bakan da ka ja.
13 Ka sami ɗaukaka, ya Ubangiji cikin ƙarfinka;
za mu rera mu kuma yabi ikonka.
1 Ana nan, sai Nahash sarkin Ammonawa ya mutu, sai ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki. 2 Dawuda ya yi tunani, “Zan nuna jinƙai ga Hanun ɗan Nahash, domin mahaifinsa ya nuna alheri gare ni.” Saboda haka Dawuda ya aika da tawaga don yă yi wa Hanun ta’aziyya game da mahaifinsa.
Sa’ad da mutanen Dawuda suka iso wurin Hanun a ƙasar Ammonawa don su ta’azantar da shi, 3 sai manyan Ammonawa suka ce wa Hanun, “Kana tsammani Dawuda yana girmama mahaifinka ne da ya aika mutanen nan wurinka su ta’azantar da kai? Ba mutanensa sun zo ne su bincika su kuma leƙi ƙasar su tumɓuke ta ba?” 4 Saboda haka Hanun ya kama mutanen Dawuda, ya yi musu aski, ya yayyanka rigunansu a daidai ɗuwawunsu, sa’an nan ya sallame su.
5 Da wani ya zo ya faɗa wa Dawuda game da mutanen, sai ya aiki ’yan aika su sadu da su, gama an ƙasƙantar da su ainun. Sarki ya ce, “Ku zauna a Yeriko har sai gemunku sun yi girma, sa’an nan ku dawo.”
6 Sa’ad da Ammonawa suka gane cewa sun zama abin wurin a kafan hancin Dawuda, Hanun da Ammonawa suka aika da talenti dubu na azurfa don su yi haya da kekunan yaƙi da mahayan kekunan yaƙi daga Aram-Naharayim, Aram Ma’aka da Zoba. 7 Suka yi hayar kekunan yaƙi da mahayan kekunan yaƙi dubu talatin da biyu, da kuma sarkin Ma’aka tare da mayaƙansa, waɗanda suka zo suka kafa sansani kusa da Medeba, yayinda Ammonawa suka tattaru daga garuruwansu suka fita yaƙi.
8 Da jin haka, Dawuda ya aiki Yowab tare da dukan mayaƙa masu yaƙi. 9 Ammonawa suka fito suka ja dāgā a ƙofar birninsu, yayinda sarakunan da suka zo, su kansu suka ware suna a fili.
10 Yowab ya ga cewa akwai dāgā a gabansa da bayansa; sai ya zaɓi waɗansu mayaƙa mafi kyau a Isra’ila ya sa su a kan Arameyawa. 11 Ya sa sauran mutanen a ƙarƙashin kulawar Abishai ɗan’uwansa, aka sa a kan Ammonawa. 12 Yowab ya ce, “In Arameyawa suka fi ni ƙarfi, sai ka kawo mini ɗauke da ni; amma in Ammonawa sun fi ka ƙarfi, sai in kawo maka ɗauke. 13 Ka yi ƙarfin hali bari mu yi yaƙi da jaruntaka saboda mutanenmu da biranen Allahnmu. Ubangiji zai yi abin da ya ga ya yi masa kyau.”
14 Sai Yowab da ƙungiyoyin mayaƙan da suke tare da shi suka matso don su yi yaƙi da Arameyawa, Arameyawan kuwa suka gudu a gabansa. 15 Sa’ad da Ammonawa suka ga Arameyawa suna gudu, sai su ma suka guda a gaban ɗan’uwansa Abishai suka shiga cikin birni. Sai Yowab ya koma Urushalima.
16 Bayan Arameyawa suka ga cewa Isra’ila sun ci su da yaƙi, sai suka aiki ’yan aika suka sa aka kawo Arameyawan da suke hayen Kogi waɗanda Shobak shugaban mayaƙan Hadadezer yake shugabanta.
17 Sa’ad da aka faɗa wa Dawuda wannan, sai tattara dukan Isra’ila ya haye Urdun; ya tafi wurinsu ya kuwa ja dāgā ɗaura da su. Dawuda ya ja dāgārsa don yă sadu da Arameyawa a yaƙi, su kuwa suka yi yaƙi da shi. 18 Amma Arameyawa suka gudu a gaban Isra’ila, mutanen Dawuda kuwa suka kashe masu hawan keken yaƙinsu dubu bakwai da sojojin ƙasa dubu arba’in. Ya kuma kashe Shobak shugaban mayaƙansu.
19 Da abokan tarayyar Hadadezer suka ga Isra’ila sun ci su da yaƙi, sai suka nemi salama da Dawuda suka kuma zama bayinsa.
Saboda haka Arameyawa ba su ƙara yarda su taimaki Ammonawa ba.