Zinar Dawuda (continued)

1035 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Zabura 103

Ta Dawuda.

1 Yabi Ubangiji, ya raina;

dukan abin da yake cikin cikina, yabi sunansa mai tsarki.

2 Yabi Ubangiji, ya raina,

kada kuma ka manta dukan alheransa,

3 wanda yake gafarta dukan zunubai

yake kuma warkar da dukan cututtuka,

4 wanda ya fanshi ranka daga rami

ya naɗa maka rawani da ƙauna da kuma tausayi,

5 Wanda ya ƙosar da kai da abubuwa masu kyau

domin a sabunta ƙuruciyarka kamar na gaggafa.

6 Ubangiji yana aikata adalci

da kuma gaskiya ga duk waɗanda aka danne.

7 Ya sanar da hanyoyinsa wa Musa,

ayyukansa ga mutanen Isra’ila.

8 Ubangiji mai tausayi ne da kuma alheri,

mai jinkirin fushi, cike da ƙauna.

9 Ba zai yi ta zargi ba

ba kuwa zai yi ta jin fushi har abada ba;

10 ba ya yin da mu gwargwadon zunubanmu

ko yă sāka mana bisa ga laifofinmu.

11 Gama kamar yadda sammai suke can bisa duniya,

haka girmar ƙaunarsa yake wa masu tsoronsa;

12 kamar yadda gabas yake daga yamma,

haka ya cire laifofinmu daga gare mu.

13 Kamar yadda mahaifi yake jin tausayin ’ya’yansa,

haka Ubangiji yake jin tausayin waɗanda suke tsoronsa;

14 gama ya san yadda aka yi mu,

ya tuna cewa mu ƙura ne.

15 Game da mutum dai, kwanakinsa suna kamar ciyawa

da suke haɓaka kamar fure a gona;

16 iska kan hura a kansa sai ya ɓace

ba a kuwa sāke tuna da inda dā yake.

17 Amma daga madawwami zuwa madawwami

ƙaunar Ubangiji tana tare da waɗanda suke tsoronsa,

adalcinsa kuma tare da ’ya’yansu,

18 tare da waɗanda suke kiyaye alkawarinsa

suna kuma tuna su yi biyayya da farillansa.

19 Ubangiji ya kafa kursiyinsa a sama,

masarautarsa kuwa na mulki a bisa duka.

20 Yabi Ubangiji, ku mala’ikunsa,

ku jarumawa masu yi masa aiki,

waɗanda suke yin biyayya da maganarsa.

21 Yabi Ubangiji, dukanku rundunarsa ta sama,

ku bayinsa waɗanda kuke aikata nufinsa.

22 Yabi Ubangiji, dukanku ayyukansa

ko’ina a mulkinsa.

Yabi Ubangiji, ya raina.

2 Sama’ila 12:16–23

16 Dawuda ya roƙi Allah saboda yaron. Ya yi azumi, ya kuma shiga gidansa ya kwana kwance a ƙasa. 17 Dattawan iyalinsa suka tsaya kusa da shi don su ɗaga shi daga ƙasa, amma ya ƙi, bai kuwa ci wani abu tare da su ba.

18 A rana ta bakwai sai yaron ya rasu. Barorin Dawuda suka ji tsoro su gaya masa cewa yaron ya mutu, gama sun yi tunani cewa, “Yayinda yaron yake da rai, mun yi magana da Dawuda bai ji mu ba. Yaya za mu gaya masa yaron ya mutu? Ai, zai yi wa kansa ɓarna.”

19 Dawuda ya gane bayinsa suna wa juna raɗan wani abu, sai ya gane yaron ya mutu. Sai ya ce, “Yaron ya rasu ko?”

Suka ce, “I, ya rasu.”

20 Sa’an nan Dawuda ya tashi daga ƙasa. Bayan ya yi wanka, ya shafa mai, ya kuma canja rigunarsa, sa’an nan ya shiga gidan Ubangiji ya yi sujada. Sai ya tafi gidansa, ya nemi a ba shi abinci, aka ba shi, ya kuwa ci.

21 Barorinsa suka ce masa, “Me ya sa kake yin haka? Yayinda yaron yake da rai, ka yi azumi, ka kuma yi kuka, amma yanzu da yaron ya mutu, ka tashi, ka kuma ci abinci!”

22 Ya ce musu, “Yayinda yaron yake da rai, na yi azumi, na kuma yi kuka. Na yi tunani na ce, ‘Wa ya sani? Ko Ubangiji zai yi mini alheri yă bar yaron yă rayu.’ 23 Amma yanzu da ya mutu, me zai sa in yi azumi? Zan iya dawo da shi ne? Ni zan je wajensa, ba shi zai dawo wurina ba.”

2 Sama’ila 12:26–31

26 Ana cikin haka, sai Yowab ya yi yaƙi da Rabba na Ammonawa, ya kuma ƙwace babban birnin. 27 Sa’an nan Yowab ya aika manzanni wurin Dawuda yana cewa, “Na yaƙi Rabba na kuma ƙwace hanyar samun ruwanta. 28 Yanzu fa ka tattara saura rundunoni ka fāɗa wa birnin ka ci shi. In ba haka ba zan karɓe birnin, a kuma kira shi da sunana.”

29 Saboda haka Dawuda ya tattara sauran rundunar sojojin suka tafi Rabba suka fāɗa masa suka kuma ci shi. 30 Ya ɗauke rawanin daga kan sarkinsu, nauyinsa ya kai talenti, na zinariya, an kuma yi masa ado da duwatsu masu daraja, aka aza shi a kan Dawuda. Ya kuma kwashe ganima mai yawa daga garin. 31 Ya fito da mutanen da suke a can, ya sa su su yi aiki da zarto, da diga, da kuma gatari, ya kuma sa su bugan bulok. Haka ya yi wa dukan garuruwan Ammonawa. Sa’an nan Dawuda da dukan sojoji suka koma Urushalima.

1 Tarihi 20:2–3

2 Dawuda ya ɗauki rawani daga kan sarkinsu, nauyinsa ya kai talenti na zinariya, aka kuma yi masa ado da duwatsu masu daraja, sai Dawuda kuwa ya sa a kansa. Ya kuma kwashi ganima mai yawa daga birnin 3 ya kuma fitar da mutanen da suke can, ya sa su aiki da zartuna da makamai masu kaifi da kuma gatura. Dawuda ya yi haka da dukan garuruwan Ammonawa. Sa’an nan Dawuda da mayaƙansa gaba ɗaya suka koma Urushalima.