An Naɗa Dawuda Sarki a kan Dukan Isra’ila
1048 kafin haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
1 Dukan kabilar Isra’ila suka zo wurin Dawuda a Hebron suka ce, “Mu nama da jininka ne. 2 A dā da Shawulu yake sarauta a bisanmu, kai ne kake bi Isra’ilawa zuwa yaƙe-yaƙensu. Ubangiji kuwa ya ce maka, ‘Za ka zama makiyayi mutanena Isra’ila, za ka kuma zama sarkinsu.’ ”
3 Sa’ad da dukan dattawan Isra’ila suka zo wurin Sarki Dawuda a Hebron, sarki ya yi yarjejjeniya da su a gaban Ubangiji, suka kuwa naɗa Dawuda sarki bisa Isra’ila.
1 Sai Dawuda ya tattauna da kowane ɗaya daga cikin shugabanninsa, shugabannin sojoji na dubu-dubu da na ɗari-ɗari. 2 Sa’an nan ya ce wa dukan taron Isra’ila, “In ya yi muku kyau kuma in nufin Ubangiji Allahnmu ne, bari mu aika da saƙo nesa da kuma ko’ina zuwa ga sauran ’yan’uwanmu a duk iyakokin Isra’ila, da kuma zuwa ga firistoci da Lawiyawa waɗanda suke tare da su a garuruwansu da makiyayansu, su zo wurinmu. 3 Bari mu ɗauko akwatin alkawarin Allahnmu mu kawo wurinmu, gama ba mu neme shi a lokacin mulkin Shawulu ba.” 4 Dukan taron jama’a suka yarda su yi haka, domin ya yi daidai ga dukan mutane.
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Zabura ce.
1 Ya Ubangiji, ka bincike ni
ka kuwa san ni.
2 Ka san sa’ad da na zauna da sa’ad da na tashi;
ka san tunanina daga nesa.
3 Ka san fitata da kuma kwanciyata;
ka saba da dukan hanyoyina.
4 Kafin in yi magana da harshena
ka santa gaba ɗaya, ya Ubangiji.
5 Ka kewaye ni, gaba da baya;
ka sa hannunka a kaina.
6 Irin wannan sanin game da ni ya fi ƙarfin magana,
ya fi ƙarfi in gane.
7 Ina zan tafi daga Ruhunka?
Ina zan gudu in tafi daga gabanka?
8 In na haura zuwa sammai, kana a can;
in na yi gado a zurfafa, kana a can.
9 In na tashi a fikafikan safiya,
in na sauka a gefe mai nisa na teku,
10 can ma hannunka zai bishe ni,
hannunka na dama zai riƙe ni gam.
11 In na ce, “Tabbatacce duhu zai ɓoye ni
haske kuma zai zama dare kewaye da ni,”
12 duhu ma ba zai zama duhu gare ka ba;
dare zai haskaka kamar rana,
gama duhu ya yi kamar haske gare ka.
13 Gama ka halicci ciki-cikina;
ka gina ni gaba ɗaya a cikin mahaifar mahaifiyata.
14 Ina yabonka domin yadda ka yi ni abin tsoro ne da kuma abin mamaki;
ayyukanka suna da banmamaki,
na san da haka sosai.
15 Ƙasusuwana ba a ɓoye suke a gare ka ba
sa’ad da aka yi ni asirce.
Sa’ad da saƙa ni gaba ɗaya a zurfafan duniya.
16 Idanunka sun ga jikina marar fasali;
dukan kwanakin da aka tsara mini a rubuce suke a littafinka
kafin ɗayansu yă kasance.
17 Tunaninka suna da daraja gare ni, ya Allah!
Yawansu ba su da iyaka!
18 A ce zan iya ƙirgansu,
za su fi yashin teku yawa.
Sa’ad da na farka, ina nan tare da kai har yanzu.
19 Da kawai za ka kashe mugaye, ya Allah!
Ku rabu da ni, ku masu kisankai!
20 Suna magana game da kai da mugun nufi;
maƙiyanka suna ɗaukan sunanka a banza.
21 Ba ina ƙin masu ƙinka ba, ya Ubangiji,
ina kuma ƙyamar waɗanda suke tayar maka ba?
22 Ba ni da wani abu da nake musu sai kiyaye kawai;
na ɗauke su abokan gābana.
23 Ka bincike ni, ya Allah ka kuma san zuciyata;
ka gwada ni ka kuma san damuwata.
24 Duba ko akwai wani laifi a cikina,
ka bishe ni a madawwamiyar hanya.
23 Ga yawan mutanen shiryayyu don yaƙi waɗanda suka zo wurin Dawuda a Hebron don su mai da mulkin Shawulu gare shi, yadda Ubangiji ya faɗa.
24 Mutanen Yahuda, masu riƙe garkuwa da māshi, su 6,800 shiryayyu don yaƙi;
25 mutanen Simeyon, jarumawa shiryayyu don yaƙi, su 7,100;
26 mutanen Lawi, su 4,600, 27 haɗe da Yehohiyada, shugaban iyalin Haruna tare da mutane 3,700, 28 da Zadok, matashi jarumi sosai, tare da shugabanni su 22 daga iyalinsa;
29 mutanen Benyamin, ’yan’uwan Shawulu, su 3,000, yawanci waɗanda suke biyayya ga gidan Shawulu sai lokacin;
30 mutanen Efraim, jarumawa, sanannu cikin gidajensu, su 20 800;
31 mutanen rabin kabilar Manasse, sanannu da sunaye suka zo suka mai da Dawuda sarki, su 18,000;
32 mutanen Issakar, masu fahimtar lokuta suka kuma san abin da ya kamata Isra’ila ya yi, manya 200, tare da danginsu a ƙarƙashin shugabancinsu;
33 mutanen Zebulun, ƙwararru sojoji shiryayyu don yaƙi da kowane irin makami, suka zo don su taimaki Dawuda da zuciya ɗaya, su 50,000;
34 mutanen Naftali su 1,000 shugabanni, tare da mutane 37,000 masu riƙe garkuwa da masu;
35 mutanen Dan, shiryayyu don yaƙi, su 28,600;
36 mutanen Asher, ƙwararrun sojoji shiryayyu don yaƙi, su 40,000;
37 kuma daga gabashin Urdun, mutanen Ruben, Gad da kuma rabin kabilar Manasse, masu kayan yaƙi iri-iri, su 120,000.
38 Dukan waɗannan mayaƙa ne waɗanda suka ba da kansu da yardar rai su yi hidima.
Suka zo Hebron da cikakken niyya don su naɗa Dawuda sarki a bisa dukan Isra’ila. Duka sauran Isra’ilawa su ma suka goyi baya a naɗa Dawuda sarki. 39 Mutanen suka yi kwana uku a can tare da Dawuda, suna ci suna sha, gama iyalansu sun yi musu tanadi. 40 Haka ma, maƙwabtansu daga nesa har Issakar, Zebulun da Naftali suka zo suka kawo abinci a kan jakuna, raƙuma, alfadarai da shanu. Akwai tanadin mai yawa na gari, kauɗar ɓaure, nonnan busassun ’ya’yan inabi, ruwan inabi, mai, shanu da tumaki. Duk an yi haka don a nuna farin ciki ƙwarai a cikin dukan ƙasar Isra’ila.
8 Waɗannan su ne sunayen jarumawan Dawuda.
Yosheb-Basshebet, mutumin Takemon ɗaya daga cikin shugabanni Uku; ya ɗaga māshinsa ya kashe mutum ɗari takwas a lokaci guda.
9 Na biye da shi a matsayi cikin jarumawa ukun nan, shi ne Eleyazar ɗan Dodo, mutumin Aho. Eleyazar ya kasance tare da Dawuda sa’ad da suka fuskanci Filistiyawa waɗanda suka taru a Fas Dammim don yaƙi. Mutanen Isra’ila suka gudu, 10 amma ya yi tsayi daka, ya bugi Filistiyawa sai da hannunsa ya gaji har ya liƙe wa māshinsa. Ubangiji kuwa ya sa aka yi babban nasara a ranar. Sauran sojoji suka komo wurin Eleyazar, don kawai su washe ganima.
11 Na biye da Agiyi a matsayi, shi ne Shamma ɗan Agi, mutumin Harar. Sa’ad da Filistiyawa suka taru a wani wurin da take gona cike da waken barewa, sai rundunar Isra’ila suka gudu daga Filistiyawa. 12 Amma Shamma ya yi tsayi daka a tsakiyar gonar. Ya kāre ta, ya kuma bugi Filistiyawa, Ubangiji kuwa ya sa aka yi babban nasara.
20 Abishai ɗan’uwan Yowab shi ma babba ne cikin Ukun nan. Ya ɗaga māshinsa a kan mutum ɗari uku, waɗanda ya kashe, ya kuma zama sananne kamar Ukun. 21 Aka ninka girmama shi bisa Ukun, sai ya zama shugaba, ko da yake ba a haɗa shi a cikinsu ba.
22 Benahiya ɗan Yehohiyada shi ma wani barden yaƙi ne daga Kabzeyel, wanda ya yi manyan abubuwa. Ya bugi gwanayen Mowab biyu. Ya kuma gangara zuwa cikin rami a ranar da aka yi dusar ƙanƙara ya kashe zaki. 23 Ya kuma kashe wani mutumin Masar mai tsayi ƙafa bakwai da rabi. Ko da yake mutumin Masar yana da māshi kamar sandan masaƙa a hannunsa, Benahiya ya yaƙe shi da kulki. Ya ƙwace māshin daga hannun mutumin Masar ya kuma kashe shi da māshin nan nasa. 24 Irin abubuwan da Benahiya ɗan Yehohiyada ya yi ke nan; shi ma sananne ne kamar waɗannan jarumawa uku. 25 Aka ɗauka shi da bangirma fiye da Talatin nan, amma ba a haɗa shi cikin Ukun ba. Dawuda kuwa ya sa shi yă lura da masu tsaron lafiyarsa.
26 Jarumawan nan su ne,
Asahel ɗan’uwan Yowab,
Elhanan ɗan Dodo daga Betlehem,
27 Shammot mutumin Haror,
Helez mutumin Felon,
28 Ira ɗan Ikkesh daga Tekowa,
Abiyezer daga Anatot,
29 Sibbekai mutumin Husha,
Ilai mutumin Aho,
30 Maharai mutumin Netofa,
Heled ɗan Ba’ana mutumin Netofa,
31 Ittai ɗan Ribai daga Gibeya a Benyamin,
Benahiya mutumin Firaton,
32 Hurai daga kogunan Ga’ash,
Abiyel mutumin Arba,
33 Azmawet mutumin Harum,
Eliyaba mutumin Sha’albo,
34 ’ya’yan Hashem mutumin Gizon maza,
Yonatan ɗan Shageye mutumin Harar,
35 Ahiyam ɗan Sakar mutumin Harar,
Elifal ɗan Ur,
36 Hefer mutumin Mekerat,
Ahiya mutumin Felon,
37 Hezro mutumin Karmel,
Na’arai ɗan Ezbai,
38 Yowel ɗan’uwan Natan,
Mibhar ɗan Hagiri,
39 Zelek mutumin Ammon
Naharai Baroti, mai ɗaukar kayan yaƙin Yowab ɗan Zeruhiya,
40 Ira mutumin Itra,
Gareb mutumin Itra,
41 Uriya mutumin Hitti
Zabad ɗan Alai,
42 Adina ɗan Shiza mutumin Ruben, wanda shi ne babba na mutanen Ruben, kuma talatin suna tare da shi,
43 Hanan ɗan Ma’aka,
Yoshafat mutumin Mit,
44 Uzziya mutumin Ashtarot,
Shama da Yehiyel ’ya’yan Hotam mutumin Arower maza,
45 Yediyayel ɗan Shimri,
ɗan’uwansa Yoha mutumin Tiz,
46 Eliyel mutumin Ma’aha,
Yeribai da Yoshawiya ’ya’yan Elna’am maza,
Itma mutumin Mowab,
47 Eliyel, Obed da Ya’asiyel mutumin Mezob.
4 Dawuda yana da shekara talatin ɗaya sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara arba’in. 5 A Hebron ya yi mulki a bisa Yahuda shekara bakwai da wata shida, a Urushalima kuma ya yi mulki a bisa Isra’ila da Yahuda shekara talatin da uku.
6 Sarki da mutanensa suka tafi Urushalima don su kai wa Yebusiyawan da suke zaune a can hari, Yebusiyawa suka ce wa Dawuda, “Ba za ka shiga nan ba; ko makafi da guragu kaɗai ma za su kore ka.” Suka yi tsammani suna cewa, “Dawuda ba zai iya shiga can ba.” 7 Duk da haka, Dawuda ya kame kagarar Sihiyona, wadda ta zama Birnin Dawuda.
8 A ranar, Dawuda ya ce, “Duk wanda zai kame Yebusiyawa, dole yă yi amfani da wuriyar ruwa don yă kai ga waɗannan ‘guragu da makafi’ waɗanda suke abokan gāban Dawuda.” Shi ya sa suka ce, “ ‘Makafi da guragu’ ba za su shiga fadan sarki ba.”
9 Sai Dawuda ya zauna a kagarar, ya kuma kira ta Birnin Dawuda. Ya gina wuraren da suke kewaye da ita, tun daga madogaran gini zuwa ciki. 10 Ya yi ta ƙara ƙarfi, gama Ubangiji Allah Maɗaukaki yana tare da shi.
1 Dukan Isra’ila fa suka taru wurin Dawuda a Hebron suka ce, “Mu jiki da jininka ne. 2 A dā, ko a lokacin da Shawulu yake sarki, ai, kai ne kake shugabantar Isra’ila a yaƙe-yaƙe. Kuma Ubangiji Allahnka ya ce maka, ‘Za ka zama makiyayin mutanena Isra’ila, za ka kuma zama mai mulkinsu.’ ”
3 Sa’ad da dukan dattawan Isra’ila suka zo wurin Sarki Dawuda a Hebron, suka yi yarjejjeniya da shi a gaban Ubangiji, suka kuwa shafe Dawuda ya zama sarki a bisa Isra’ila, yadda Ubangiji ya yi alkawari ta wurin Sama’ila.
4 Dawuda tare da dukan Isra’ilawa suka taka zuwa Urushalima (wato, Yebus). Yebusiyawan da suke zama a wurin 5 suka ce wa Dawuda, “Ba za ka shiga nan ba.” Duk da haka, Dawuda ya ci kagarar Sihiyona, Birnin Dawuda.
6 Dawuda ya ce, “Duk wanda ya jagoranci yaƙi a kan Yebusiyawa zai zama babban shugaban mayaƙa.” Yowab ɗan Zeruhiya ya fara haurawa, ta haka ya zama shugaba.
7 Dawuda zauna a kagarar, ta haka aka kira ta Birnin Dawuda. 8 Sai ya gina birni kewaye da shi, daga madogaran gini zuwa katangar da take kewaye, yayinda Yowab ya maido da sauran birnin. 9 Dawuda kuwa ya ƙara ƙarfi, domin Ubangiji Maɗaukaki yana tare da shi.
10 Waɗannan su ne manyan jarumawan Dawuda, su ne, tare da dukan Isra’ila, suka ba wa mulkinsa goyon baya mai ƙarfi da ya kai bisa dukan ƙasar, yadda Ubangiji ya yi alkawari. 11 Ga jerin sunayen jarumawan Dawuda.
Yashobeyam wani ɗan Hakmoni, shi ne babban shugaba; ya ɗaga māshinsa a kan mutum ɗari uku, waɗanda ya kashe a ƙarawa guda kawai.
12 Biye da shi, shi ne Eleyazar ɗan Dodo mutumin Aho, ɗaya daga cikin jarumawa uku. 13 Yana tare da Dawuda a Fas Dammim sa’ad da Filistiyawa suka taru can don yaƙi. A wani wuri inda akwai gona cike da sha’ir, sojoji suka gudu daga Filistiyawa. 14 Sai shi da Dawuda suka shiga gonar sha’ir ɗin, suka tsaya ciki don su tsare ta. Suka ragargaza Filistiyawa, Ubangiji kuma ya kawo babban nasara.
18 Abishai, ɗan’uwan Yowab, ɗan Zeruhiya shi shugaban Ukun nan. Ya ɗauki māshinsa ya kashe mutane ɗari uku, ta haka ya zama sananne kamar Ukun nan. 19 Ashe, ba a girmama shi fiye da Ukun ba? Ya zama komandansu, ko da yake ba a haɗa shi a cikinsu ba.
20 Benahiya, ɗan Yehohiyada mutumin Kabzeyel shi ma jarumi ne sosai, ya yi nasarori masu yawa. Ya bugi ƙwararrun jarumawan Mowab guda biyu. Ya kuma shiga rami wata ranar da ake ƙanƙara, ya kashe zaki. 21 Ya kuma buge wani jibgaggen mutumin Masar. Duk da māshin da mutumin Masar yana riƙe a hannunsa, Benahiya ya kai masa hari da kulki. Ya ƙwace māshin daga hannunsa, ya kuma kashe shi da māshin. 22 Irin nasarorin da Benahiya ɗan Yehohiyada ya yi ke nan; shi ma jarumi ne sosai kamar jarumawan nan uku. 23 Aka fi ba shi girma fiye da talatin ɗin nan, amma ba ya cikin ukun. Dawuda ya sa shi yă zama ɗaya daga cikin masu tsaron lafiyarsa.
24 Cikin talatin ɗin kuwa akwai,
Asahel, ɗan’uwan Yowab,
Elhanan, ɗan Dodo mutumin Betlehem,
25 Shamma, mutumin Harod,
Elika, mutumin Harod,
26 Helez, mutumin Falti,
Ira, ɗan Ikkesh mutumin Tekowa,
27 Abiyezer, mutumin Anatot, da
Mebunnai, mutumin Husha,
28 Zalmon, mutumin Aho,
da Maharai, mutumin Netofa,
29 Heleb, ɗan Ba’ana daga Netofa,
Ittai, ɗan Ribai mutumin Gibeya a Benyamin,
30 Benahiya, mutumin Firaton,
da Hiddai, daga rafuffukan Ga’ash,
31 Abi-Albon, mutumin Arba, da
Azmawet, mutumin Bahurim,
32 Eliyaba, mutumin Sha’albo,
’Ya’yan Yashen,
Yonatan, 33 ɗan Shamma mutumin Harar,
da Ahiyam, ɗan Sharar mutumin Harod.
34 Elifelet, ɗan Ahasbai mutumin Ma’aka,
Eliyam, ɗan Ahitofel mutumin Gilo,
35 Hezro, mutumin Karmel,
Fa’arai, mutumin Arbi,
36 Igal, ɗan Natan mutumin Zoba,
ɗan Hagiri,
37 Zelek, mutumin Ammon
Naharai, mutumin Beyerot mai ɗaukan wa Yowab, ɗan Zeruhiya makamai,
38 Ira, mutumin Itra.
Gareb, mutumin Itra,
39 da kuma Uriya, mutumin Hitti.
Su talatin da bakwai ne duka.