Sairus Ya Ba da Umarnin Maido da Yahudawa
536 kafin haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
1 A shekara ta farko ta mulkin sarkin Farisa, wato, sarki Sairus, domin a cika maganar Ubangiji da aka yi ta bakin Irmiya, sai Ubangiji ya taɓa zuciyar Sairus sarkin Farisa ya yi shela a duk fāɗin ƙasarsa, ya kuma rubuta cewa,
2 “Ga abin da Sairus sarkin Farisa yake shela,
“ ‘Ubangiji Allah na sama ya ba ni iko in yi mulkin duniya duka, ya kuma zaɓe ni in gina masa haikali a Urushalima cikin Yahuda. 3 Duk wanda yake nasa a cikinku bari Allahnsa yă kasance tare da shi, bari yă tafi Urushalima cikin Yahuda yă gina haikalin Ubangiji, Allah na Isra’ila, Allah wanda yake a Urushalima. 4 Duk inda akwai mutumin Yahuda da ya rage, sai mutanen da suke zama kusa da shi, su taimake shi da azurfa, da zinariya, da kaya, da kuma dabbobi, tare da kyautai na yardar rai saboda Gidan Allah wanda yake a Urushalima.’ ”
Waƙar haurawa.
1 Sa’ad da Ubangiji ya dawo da kamammu zuwa Sihiyona,
mun kasance kamar mutanen da suka yi mafarki.
2 Bakunanmu sun cika da dariya,
harsunanmu da waƙoƙin farin ciki.
Sai ana faɗi a cikin al’ummai,
“Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominsu.”
3 Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominmu,
mun kuwa cika da farin ciki.
4 Ka maido da wadatarmu, ya Ubangiji
kamar rafuffuka a Negeb.
5 Waɗanda suka yi shuka da hawaye
za su yi girbi da waƙoƙin farin ciki.
6 Shi da ya fita yana kuka,
riƙe da iri don shuki,
zai dawo da waƙoƙin farin ciki,
ɗauke da dammuna.
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Na ’ya’yan Kora maza. Zabura ce.
1 Ka nuna wa ƙasarka alheri, ya Ubangiji;
ka mai da nasarorin Yaƙub.
2 Ka gafarta laifin mutanenka
ka kuma shafe dukan zunubansu. Sela
3 Ka kau da dukan fushinka
ka kuma juye daga hasalar fushinka.
4 Ka sāke mai da mu, ya Allah Mai Cetonmu,
ka kau da rashin jin daɗinka daga gare mu.
5 Za ka ci gaba da fushi da mu har abada ne?
Za ka ja fushinka cikin dukan tsararraki?
6 Ba za ka sāke raya mu ba,
don mutanenka su yi farin ciki a cikinka?
7 Ka nuna mana ƙaunarka marar ƙarewa, ya Ubangiji,
ka kuma ba mu cetonka.
8 Zan saurari abin da Allah Ubangiji zai faɗa;
ya yi alkawarin salama ga mutanensa, tsarkakansa,
amma kada su koma ga wauta.
9 Tabbatacce cetonsa yana kusa da waɗanda suke tsoronsa,
don ɗaukakarsa ta zauna a cikin ƙasarmu.
10 Ƙauna da aminci za su sadu;
adalci da salama za su yi wa juna sumba.
11 Aminci zai ɓulɓulo daga ƙasa,
adalci kuma yă duba daga sama.
12 Ubangiji tabbatacce zai bayar da abin da yake da kyau,
ƙasarmu kuwa za tă ba da amfaninta.
13 Adalci na tafiya a gabansa
yana shirya hanya domin ƙafafunsa.
22 Don a cika maganar da Ubangiji ya yi ta wurin Irmiya, a shekara farko ta Sairus sarkin Farisa, sai Ubangiji ya motsa zuciyar Sairus na Farisa don yă yi shela a dukan masarautarsa, ya kuma sa shi a rubuce cewa,
23 “Ga abin da Sairus sarkin Farisa ya ce,
“ ‘Ubangiji Allah na sama, ya ba ni dukan mulkokin duniya, ya kuma naɗa ni in gina masa haikali a Urushalima a Yahuda. Duk wani na mutanensa a cikinku, bari yă haura yă tafi, bari kuma Ubangiji Allahnsa yă kasance tare da shi.’ ”