Bala’am da Balak (continued)

1451 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Ƙidaya 24

1 To, da Bala’am ya ga cewa Ubangiji yana jin daɗin sa wa Isra’ila albarka, bai koma wajen sihiri kamar dā ba, amma ya juya fuskarsa wajen hamada. 2 Da Bala’am ya duba sai ya ga Isra’ila sun yi sansani kabila, kabila, Ruhun Allah kuwa ya sauko masa, 3 sai ya yi annabcinsa ya ce,

“Maganar Bala’am ɗan Beyor,

saƙon mutumin da idanunsa ke gani sarai,

4 maganar mutumin da ya saurari maganar Allah,

maganar wanda yake ganin wahayi daga Maɗaukaki,

mutumin da ya fāɗi rubda ciki, wanda kuma idanunsa suna a buɗe.

5 “Ina misalin kyan tentunanka, ya Yaƙub,

wuraren zamanka, ya Isra’ila!

6 “Kamar kwaruruka suke a shimfiɗe,

kamar lambu kusa da rafi,

kamar itatuwan aloyes da Ubangiji ya dasa,

kamar itatuwa al’ul kusa da ruwaye.

7 Ruwa zai kwararo daga bokitinsu;

irinsu za su sami ruwa a yalwace.

“Sarkinsu zai fi sarkin Agag;

mulkinsu zai ɗaukaka.

8 “Allah ya fitar da su daga Masar;

suna da ƙarfin kutunkun ɓauna.

Sun cinye abokan gāban,

suka kakkarya ƙasusuwansu;

da kibiyoyinsu suka sossoke su.

9 Kamar zaki sun laɓe sun kwanta,

kamar zakanya, wa zai yi ƙarfin hali yă tashe su?

“Bari waɗanda suka albarkace ka, su sami albarka

waɗanda kuma suka la’anta ka, su la’antu!”

10 Fushin Balak ya ƙuna a kan Bala’am. Ya tafa hannunsa, ya ce masa, “Na kira ka don ka la’anta abokan gābana, amma sai ga shi ka sa musu albarka har sau uku. 11 Yanzu ka bar nan ka tafi gida! Na ce zan sāka maka da lada mai kyau, amma Ubangiji ya hana ka samun ladan.”

12 Bala’am ya ce wa Balak, “Ban faɗa wa ’yan aikan da ka aiko wurina ba cewa, 13 ‘Ko da a ce Balak zai ba ni gidansa cike da azurfa da zinariya, ba zan yi wani abu ko kaɗan saɓanin umarnin Ubangiji Allahna ba, kuma dole in faɗa abin da Ubangiji ya ce ne kawai’? 14 Yanzu zan koma wajen mutanena, amma bari in gargaɗe ka game da abin da mutanen nan za su yi wa mutanenka cikin kwanaki masu zuwa.”

15 Sa’an nan ya furta saƙonsa.

“Maganar Bala’am ɗan Beyor,

saƙon mutumin da idanunsa ke gani sarai,

16 maganar mutumin da ya saurari maganar Allah,

wanda yake da sani daga Mafi Ɗaukaka,

wanda yake ganin wahayi daga Maɗaukaki,

wanda ya fāɗi rubda ciki, wanda kuma idanunsa suna a buɗe.

17 “Na gan shi, amma ba yanzu ba;

na hange shi, amma ba kusa ba.

Tauraro zai fito daga Yaƙub;

sandan mulki zai fito daga Isra’ila.

Zai ragargaje goshin Mowab,

kawunan dukan ’ya’yan Set.

18 Za a ci Edom da yaƙi;

za a ci Seyir, abokiyar gābanta,

amma Isra’ila zai ƙara ƙarfi.

19 Mai mulki zai fito daga Yaƙub

yă hallaka waɗanda suka ragu a birnin.”

20 Sai Bala’am ya ga Amalek, ya kuma furta maganarsa.

“Amalek yana cikin al’ummai na fari,

amma zai zama na ƙarshen da za a hallaka.”

21 Sai ya ga Keniyawa, ya kuma furta maganarsa.

“Wurin zamanku lafiya yake,

an kuma sa sheƙarku a cikin duwatsu;

22 duk da haka, za a hallaka ku Keniyawa

sa’ad da Asshur ya kame ku.”

23 Sai ya furta maganarsa ya ce,

“Wayyo, wa zai rayu sa’ad da Allah ya yi haka?

24 Jiragen ruwa za su zo daga Kittim;

za su murƙushe Asshur da Eber,

amma su ma za a hallaka su.”

25 Sa’an nan Bala’am ya tashi ya koma gidan, Balak kuma ya yi tafiyarsa.

Tafiya ta arba’in da biyu: Filayen Mowab

Tafiya ta arba’in da biyu: filayen Mowab, tare da sansanin kusa da Bet-Yeshimot da Abel-Shittim.

Ƙidaya 33:49

49 A can filayen Mowab, suka yi sansani kusa da Urdun ɗaura da Bet-Yeshimot har zuwa Abel-Shittim.

Bautar Gunkin Ba’al-Feyor na Feyor

Ƙidaya 25

1 Lokacin da Isra’ila suke a sansani a Shittim, sai maza suka fara yin lalata da matan Mowabawa, 2 waɗanda suka gayyace su zuwa wajen hadayu na allolinsu. Mutane suka ci suka kuma yi wa waɗannan alloli sujada. 3 Ta haka Isra’ila suka sa kai a bautar gumaka Ba’al-Feyor. Ubangiji kuwa ya husata da su.

4 Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka kama dukan shugabannin mutanen nan, ka kashe su, ka kuma bar su a tsakar rana a gaban Ubangiji, don Ubangiji yă huce daga fushin da nake yi da Isra’ila.”

5 Saboda haka Musa ya ce wa alƙalan Isra’ila, “Dole kowannenku yă kashe mutanen nan da suka haɗa kai cikin bautar Ba’al-Feyor.”

6 Sa’an nan wani mutumin Isra’ila ya kawo wata Bamidiyana a iyalinsa a idon Musa da dukan taron jama’ar Isra’ila, yayinda suke kuka a ƙofar Tentin Sujada. 7 Da Finehas ɗan Eleyazar, ɗan Haruna, firist, ya ga haka, sai ya bar taron, ya ɗauki māshi 8 ya bi mutumin Isra’ilan nan cikin tenti, ya soke dukansu biyu, māshin ya ratsa jikin mutumin Isra’ilan har zuwa jikin macen. Sa’an nan aka tsai da annoban nan a kan Isra’ilawa. 9 Waɗanda suka mutu a wannan annoba, sun kai mutum 24,000.

10 Ubangiji ya ce wa Musa, 11 “Finehas ɗan Eleyazar, ɗan Haruna, firist, ya kawar da fushina daga Isra’ilawa; saboda ya yi kishi irin nawa a gabansu, don haka saboda ɗaukakata ban kawo ƙarshensu ba. 12 Saboda haka ka faɗa masa cewa zan yi alkawarin salama da shi. 13 Shi da zuriyarsa za su kasance da alkawari na zama firist har abada, saboda kishinsa domin ɗaukakar Allahnsa, ya kuma yi kafara domin Isra’ilawa.”

14 Sunan mutumin Isra’ilan da aka kashe tare da macen nan Bamidiyana kuwa Zimri ne, ɗan Salu, shugaban mutanen Simeyon. 15 Sunan macen nan Bamidiyana da aka kashe kuwa Kozbi ne, ’yar Zur, wani basaraken iyalin Midiyawa.

16 Ubangiji ya ce wa Musa, 17 “Ka ɗauki Midiyawa a matsayin abokan gāba, ka kuma kashe su, 18 gama sun ɗauke ku a matsayin abokan gāba, sa’ad da suka ruɗe ku a kan al’amuran Feyor da ’yar’uwarsu Kozbi ’yar shugaban Midiyawa, macen da aka kashe a annoba ta dalili Feyor.”