Akish Ya Ba Dawuda Ziklag
Dawuda ya gudu zuwa wurin Akish, sarkin Gat, wanda ya ba shi Ziklag ya zauna a ciki. Mutuwar Shawulu.
1056 kafin haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
1 Dawuda ya yi tunani a ransa ya ce, “Wata rana Shawulu zai kashe ni, abu mafi kyau da zan yi shi ne in tsere zuwa ƙasar Filistiyawa. Da haka Shawulu zai fid da zuciya ga nemana a ƙasar Isra’ila, a can kuwa zan tsira daga hannunsa.”
Zabura ta Dawuda.
1 Na yi kira gare ka, ya Ubangiji; ka zo da sauri.
Ka ji muryata sa’ad da na yi kira.
2 Bari a sa addu’ata a gabanka kamar turaren ƙonawa;
bari ɗagawa hannuwana ta zama kamar hadayar yamma.
3 Ka sa mai tsaro a bakina, ya Ubangiji;
ka yi tsaron ƙofar leɓunana.
4 Kada ka bar zuciyata ta juya ga yin abin da yake mugu,
ta sa kai ga aikata mugayen ayyuka
tare da mutane masu aikata mugunta;
kada ka bari in ci abincinsu.
5 Bari mutum mai adalci yă buge ni, alheri ne;
bar shi yă tsawata mini, mai ne a kaina.
Kaina ba zai ƙi shi ba,
duk da haka addu’ata kullum tana gāba da mugayen ayyuka.
6 Za a jefar da masu mulkinsu ƙasa daga ƙwanƙolin dutse,
mugaye kuwa za su san cewa maganata daidai ne.
7 Za su ce, “Kamar yadda mutum kan yi huda yă tsage ƙasa,
haka aka watsar da ƙasusuwanmu a bakin kabari.”
8 Amma na kafa idanuna a kanka, ya Ubangiji Mai Iko Duka;
a cikinka ina neman mafaka, kada ka miƙa ni ga mutuwa.
9 Ka kiyaye ni daga tarkon da aka sa mini,
daga tarkon da mugaye suka sa.
10 Bari mugaye su fāɗa a cikin ragarsu,
amma bari ni in zo in wuce lafiya.
2 Sai Dawuda tare da mutanensa, mutum ɗari shida suka tashi suka haye zuwa wurin Akish ɗan Mawok, sarkin Gat. 3 Dawuda da mutanensa suka zauna a Gat tare da Akish. Kowa ya kasance tare da iyalinsa. Dawuda kuwa yana tare da matansa biyu. Ahinowam daga Yezireyel da Abigiyel matar Nabal da ya mutu daga Karmel. 4 Da Shawulu ya sami labari cewa Dawuda ya gudu zuwa Gat, bai ƙara fita nemansa ba.
5 Sai Dawuda ya ce wa Akish, “In na sami tagomashi a gabanka ka ba ni wani wuri a cikin biranenka in zauna a can. Don me bawanka zai kasance tare da kai a gidan sarauta?”
6 A ranar Akish ya ba shi Ziklag wanda tun dā take ta sarkin Yahuda. 7 Dawuda ya zauna a yankin Filistiyawa shekara ɗaya da wata huɗu.
1 Waɗannan su ne mutanen da suka zo wurin Dawuda a Ziklag, yayinda aka kore shi daga gaban Shawulu ɗan Kish (suna cikin jarumawan da suka taimake shi a yaƙi; 2 suna da baka suna kuma iya harba kibiya, ko majajjawa da hannun dama ko na hagu; su ’yan’uwan Shawulu ne daga kabilar Benyamin):
3 Ahiyezer babbansu da Yowash ’ya’yan Shema’a maza daga Gibeya;
Yeziyel da Felet ’ya’yan Azmawet;
Beraka, Yehu daga Anatot, 4 da Ishmahiya daga Gibeyon, wani jarumi a cikin Talatin nan, wanda shi ne shugaban Talatin;
Irmiya, Yahaziyel, Yohanan, Yozabad daga Gedera, 5 Eluzai, Yerimot, Beyaliya, Shemariya da Shefatiya daga Haruf;
6 Elkana, Isshiya, Azarel, Yoyezer da Yashobeyam daga Kora;
7 da Yoyela da Zebadiya ’ya’yan Yeroham maza daga Gedor.
8 Dawuda da mutanensa suka haura suka yaƙi Geshurawa, da Girziyawa, da Amalekawa. (Waɗannan su ne mazaunan ƙasar a dā, tun daga Shur har zuwa ƙasar Masar.) 9 Duk lokacin da ya yaƙi wani wuri, ba ya barin namiji ko mace da rai, amma sai ya kwashe tumaki, da shanu, da jakuna, da raƙuma, da riguna, sa’an nan yă koma wurin Akish.
10 Idan Akish ya ce, “Ina ka kai hari yau?” Sai Dawuda yă ce, “Na kai hari a Negeb ta Yahuda, ko Negeb ta Yerameyel, ko Negeb na Keniyawa.” 11 Bai bar a kawo namiji ko mace da rai a Gat ba, gama yana tunani, “Za su ba da sanarwa a kanmu su ce, ‘Ga abin da Dawuda ya yi.’ ” Haka ya yi ta yi dukan rayuwarsa a ƙasar Filistiyawa. 12 Akish ya amince da Dawuda sosai, har ya ce wa kansa, “Ga shi ya mai da kansa abin ƙi ga mutanensa Isra’ilawa, zai zama bawana har abada.”
Mutuwar Shawulu 1055 kafin haihuwar Almasihu
1 Filistiyawa suka tattara sojojinsu domin su yaƙi Isra’ila. Akish ya ce wa Dawuda, “Sai ka sani fa, kai da mutanenka za ku tafi tare da ni da sojojina.”
2 Dawuda ya ce, “Kai da kanka za ka ga abin da bawanka zai yi.”
Akish ya ce, “Da kyau, zan sa ka zama mai kāre ni.”
3 Sama’ila dai ya riga ya rasu, dukan Isra’ila suka yi makokinsa suka binne shi a garinsa a Rama. Shawulu kuma ya kori duk masu duba da masu maitanci daga ƙasar.
4 Filistiyawa suka tattaru suka yi sansani a Shunem. Shawulu ya tattara dukan Isra’ila suka yi sansani a Gilbowa. 5 Da Shawulu ya ga sojojin Filistiyawa sai ya ji tsoro, ya firgita ƙwarai. 6 Ya nemi nufin Ubangiji amma bai sami amsa daga wurin Ubangiji ko ta wurin mafarki, ko ta wurin Urim, ko ta wurin annabawa ba. 7 Shawulu ya ce wa fadawansa, “Ku nemo mini wata mace mai duba domin in tafi wurinta in yi tambaya.”
Suka ce, “Akwai guda a En Dor.”
8 Sai Shawulu ya sa waɗansu tufafi ya ɓad da kama, shi da waɗansu mutum biyu suka tafi wurin matar da dare, ya ce mata, “Ki yi mini duba ta hanyar sihiri, ki hawar mini duk wanda zan faɗa miki.”
9 Amma matar ta ce masa, “Tabbatacce ka dai san abin da Shawulu ya yi, ya karkashe masu duba da masu maitanci a ƙasar. Me ya sa kake sa mini tarko, don ka sa a kashe ni?”
10 Shawulu ya rantse mata da Ubangiji. Ya ce, “Muddin Ubangiji yana a raye, ba za a hukunta ki a kan wannan ba.”
11 Sai matar ta ce, “Wa kake so in hauro maka?”
Sai ya ce, “Ki hauro mini da Sama’ila.”
12 Da matar ta ga Sama’ila sai ta yi ihu da ƙarfi ta ce wa Shawulu, “Me ya sa ka ruɗe ni? Kai ne Shawulu!”
13 Sai sarki ya ce mata, “Kada ki ji tsoro. Me kika gani?”
Matar ta ce, “Na ga wani kurwa tana fitowa daga ƙasa.”
14 Ya ce, “Yaya kamanninsa yake?”
Ta ce, “Wani tsoho sanye da taguwa ne yake haurawa.”
Shawulu ya gane cewa Sama’ila ne, sai ya rusuna da fuskarsa har ƙasa.
15 Sama’ila ya ce wa Shawulu, “Don me ka dame ni, ta wurin hauro da ni?”
Shawulu ya ce, “Ina cikin babban damuwa ce, Filistiyawa sun fāɗa mini, Allah kuma ya juya mini baya. Bai amsa mini, ko ta mafarki, ko kuma ta annabawa ba, saboda haka na kira ka don ka gaya mini abin yi.”
16 Sama’ila ya ce, “Don me kake tambayata bayan Ubangiji ya rabu da kai? Ya zama maƙiyinka? 17 Ubangiji ya cika abin da ya yi magana ta wurina. Ubangiji ya fizge mulki daga hannunka, ya ba maƙwabcinka Dawuda. 18 Gama ba ka yi biyayya ga Ubangiji ba, ba ka zartar da hukuncinsa mai zafi a kan Amalekawa ba. Saboda haka Ubangiji ya yi maka haka yau. 19 Ubangiji zai ba da Isra’ila da kuma kai ga Filistiyawa, gobe kuwa da kai da ’ya’yanka za ku kasance tare da ni. Ubangiji kuma zai ba da sojojin Isra’ila a hannun Filistiyawa.”
20 Da jin maganar Sama’ila sai Shawulu ya faɗi ƙasa warwas. Tsoro ya kama shi ƙwarai. Ba shi kuma da ƙarfi domin bai ci kome ba dukan yini da kuma dukan dare.
21 Da matar ta zo wurin Shawulu, ta ga shi a firgice, sai ta ce masa, “Duba baranyarka ta yi maka biyayya ta yi kasai da ranta, ta yi abin da ka ce ta yi. 22 To, kai ma ka kasa kunne ga baranyarka, zan ba ka abinci ka ci don ka sami ƙarfin tafiya.”
23 Sai ya ƙi. Ya ce, “Ba zan ci abinci ba.”
Sai da bayinsa da matar suka roƙe shi, sa’an nan ya ji maganarsu, ya tashi daga ƙasa, ya zauna a bakin gado.
24 Matar kuwa tana da maraƙin da take kiwo a gida, sai ta ɗauke shi nan da nan ta yanka. Ta ɗauki garin fulawa ta kwaɓa, ta yi waina marar yisti. 25 Sai ta kawo wa Shawulu da bayinsa suka kuwa ci. A daren nan suka tashi suka tafi.