Tawayen Absalom (continued)

1027 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Zabura 62

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don Yedutun. Zaburar Dawuda.

1 Raina na samun hutu a wurin Allah ne kaɗai;

cetona na zuwa daga gare shi.

2 Shi kaɗai ne dutsena da cetona;

shi ne kagarata, ba zan jijjigu ba.

3 Har yaushe za ku tasar wa mutum guda?

Dukanku ne za ku kā da shi

wannan jinganannen bango, wannan rusasshen katanga?

4 Sun kintsa sosai su tumɓuke shi

daga matsayinsa mai martaba;

suna jin daɗi yin ƙarairayi.

Sukan sa wa mutum albarka da bakinsu,

amma a zuciyarsu la’antawa suke yi. Sela

5 Ka nemi hutu, ya raina, a wurin Allah kaɗai;

dogarata kan zo daga gare shi ne.

6 Shi ne kaɗai dutsena da cetona;

shi ne kagarata, ba zan jijjigu ba.

7 Cetona da girmata sun dangana ga Allah ne,

shi ne dutsena mai ƙarfi, mafakata.

8 Ku dogara a gare shi a duk lokuta, ya mutane;

ku faɗi albarkaci bakin zukatanku a gare shi,

gama Allah ne mafakarmu. Sela

9 Talakawa dai kamar shaƙar iska suke,

Attajirai dai kamar shirim suke;

in aka auna a ma’auni, su ba wani abu ba ne;

dukansu dai kamar shaƙar iska ne kawai.

10 Kada ku dogara a kan ƙwace

ko yin fariya a kayan sata;

ko arzikinku ya ƙaru,

kada ku sa zuciyarku a kansu.

11 Abu guda Allah ya ce,

abubuwa biyu na ji,

“Cewa kai, ya Allah, kake mai ƙarfi,

12 kuma cewa kai, ya Ubangiji, mai ƙauna ne.

Tabbatacce za ka sāka wa kowane mutum

bisa ga abin da ya yi.”

Zabura 143–144

Zabura ta Dawuda.

1 Ya Ubangiji, ka ji addu’ata,

ka saurari kukata don neman jinƙai;

cikin amincinka da adalcinka

ka amsa mini.

2 Kada ka gabatar da bawanka a gaban shari’a,

gama babu wani mai rai da yake adali a gabanka.

3 Abokin gāba yana fafarata,

ya murƙushe ni har ƙasa;

ya sa ina zama a cikin duhu

kamar waɗanda suka mutu tun tuni.

4 Ta haka ƙarfina ya ƙare a cikina

zuciyata ta damu ƙwarai.

5 Na tuna da kwanakin baya

na yi tunani a kan dukan ayyukanka

na kuma lura da abin da hannuwanka suka yi.

6 Na buɗe hannuwana gare ka;

raina yana jin ƙishinka kamar busasshiyar ƙasa. Sela

7 Ka amsa mini da sauri, ya Ubangiji;

ƙarfina ya ƙare.

Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni

in ba haka ba zan zama kamar waɗanda suka gangara zuwa rami.

8 Bari safiya ta kawo mini maganar ƙaunarka marar ƙarewa,

gama na sa zuciyata a gare ka.

Ka nuna mini hanyar da zan bi,

gama a gare ka na miƙa raina.

9 Ka cece ni daga abokan gābana, ya Ubangiji,

gama na ɓoye kaina a gare ka.

10 Ka koya mini in yi nufinka,

gama kai ne Allahna;

bari nagarin Ruhunka

yă bi da ni a ƙasar da ba gargaɗa.

11 Saboda sunanka, ya Ubangiji, ka kiyaye raina;

a cikin adalcinka, ka fid da ni daga wahala.

12 A cikin ƙaunarka marar ƙarewa, ka rufe bakunan abokan gābana;

ka hallaka dukan maƙiyana,

gama ni bawanka ne.

Ta Dawuda.

144:1 Yabo ya tabbata ga Ubangiji dutsena,

wanda ya horar da hannuwana don yaƙi,

yatsotsina don faɗa.

2 Shi ne Allah mai ƙaunata da kuma kagarata,

katangata da mai cetona,

garkuwata, wanda nake neman mafaka daga gare shi,

wanda ya sa mutane a ƙarƙashina.

3 Ya Ubangiji, wane ne mutum da ka kula da shi,

ɗan mutum da har za ka yi tunaninsa?

4 Mutum yana kama da numfashi;

kwanakinsa suna wucewa kamar inuwa.

5 Ka tsage sammanka, ya Ubangiji, ka sauko;

ka taɓa duwatsu, domin su yi hayaƙi.

6 Ka aiko da walƙiya ka watsar da abokan gāba;

ka karɓa kibiyoyinka ka sa su gudu.

7 Ka miƙa hannunka daga bisa;

ka cece ni ka kuma kuɓutar da ni

daga manyan ruwaye,

daga hannuwan baƙi

8 waɗanda bakunansu sun cika da ƙarya,

waɗanda hannuwansu na dama masu ruɗu ne.

9 Zan rera sabuwar waƙa gare ka, ya Allah;

a kan molo mai tsirkiya goma zan yi maka kiɗi,

10 ga Wannan wanda yake ba wa sarakuna nasara,

wanda ya cece bawansa Dawuda.

Daga takobin kisa. 11 Ka cece ni ka kuma kuɓutar da ni

daga hannuwan baƙi

waɗanda bakunansu sun cika da ƙarya,

waɗanda hannuwansu na dama masu ruɗu ne.

12 Ta haka ’ya’yanmu maza a ƙuruciyarsu

za su zama kamar tsire-tsiren da aka kula da su,

’ya’yanmu mata kuma za su zama kamar ginshiƙai

da sassaƙa don adon fada.

13 Rumbunanmu za su cika

da kowane irin tanadi.

Tumakinmu za su ƙaru ninki dubu,

ninki dubu goma-goma a filayenmu;

14 shanunmu za su ja kaya masu nauyi.

Ba za a sami tashin hankali a katangarmu ba,

ba zuwan zaman bauta,

ba jin kukan damuwa a titunanmu.

15 Masu albarka ne mutanen da wannan zai zama haka;

masu albarka ne mutanen da Allah ne Ubangiji.

Zabura 70

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Roƙo.

1 Ka hanzarta, ya Allah, ka cece ni;

Ya Ubangiji, zo da sauri ka taimake ni.

2 Bari masu neman raina

su sha kunya su kuma rikice;

bari dukan masu sha’awar gani lalacewata

su juye baya da kunya.

3 Bari masu ce mini, “Allah yă ƙara!”

Su juye baya saboda kunyansu.

4 Amma bari dukan masu nemanka

su yi farin ciki su kuma yi murna a cikinka;

bari waɗanda suke ƙaunar cetonka kullum su ce,

“Bari Allah yă sami ɗaukaka!”

5 Duk da haka ni matalauci ne da kuma mai bukata;

ka zo da sauri gare ni, ya Allah.

Kai ne mai taimakona da mai cetona;

Ya Ubangiji, kada ka yi jinkiri.