Wahayin Bautar Gumaka da Ta Jawo Zaman Bauta (continued)
Wahayin bautar gumaka da ta jawo zaman bauta a Babilon.
594 kafin haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
1 Na duba, sai na ga kamannin kursiyin saffaya a kan sararin da yake a bisa kawunan kerubobi. 2 Sai Ubangiji ya ce wa mutumin da yake saye da lilin, “Ka shiga cikin da’irorin da suke ƙarƙashin kerubobi. Ka cika hannuwanka da garwashin wuta wanda yake tsakanin kerubobin ka kuma watsar da su a kan birnin.” Yayinda nake dubawa, sai ya shiga.
3 Kerubobin kuwa suna tsaye a gefen kudu na haikali sa’ad da mutumin ya shiga, sai girgije ya cika filin da yake can ciki. 4 Sai ɗaukakar Ubangiji ya tashi daga bisa kerubobi ya tafi zuwa madogarar ƙofar haikali. Girgijen ya cika haikali, filin kuwa ya cika da hasken ɗaukakar Ubangiji. 5 Sai aka ji ƙarar fikafikan kerubobin har a filin waje, kamar muryar Allah Maɗaukaki sa’ad da ya yi magana.
6 Sa’ad da Ubangiji ya umarci mutumin da yake saye da lilin cewa, “Ka ɗibi wuta daga cikin tsakanin da’irorin, daga tsakanin kerubobin,” sai mutumin ya shiga ya tsaya kusa da da’irar. 7 Sa’an nan ɗaya daga cikin kerubobin ya miƙa hannu zuwa wurin wutar da take tsakaninsu. Ya ɗebo wutar daga ciki ya zuba a hannuwan mutumin da yake saye da lilin, shi kuwa ya karɓa ya fita. 8 (A ƙarƙashin fikafikan kerubobin ana iya ganin abin da ya yi kamar hannuwan mutum.)
9 Na duba, sai na ga kusa da kerubobin akwai da’irori huɗu, kowanne kusa da kerub guda; da’irorin suna ƙyalli kamar wani dutse mai daraja. 10 Game da kamanninsu kuwa, huɗu a cikinsu sun yi kama da juna; kowanne ya yi kamar da da’ira a cikin da’ira. 11 Yayinda suke tafiya, sukan tafi kowane gefe huɗun da kerubobin suka nufa; da’irorin ba sa juyawa yayinda kerubobin suke tafiya. Kerubobin suka tafi kowane gefen da kan ya nufa, ba tare da juyawa ba sa’ad da suke tafiya. 12 Jikunansu gaba ɗaya, har da bayansu, hannuwansu da fikafikansu, sun cika gaba ɗaya da idanu, kamar yadda suke a da’irori huɗun. 13 Na ji ana kiran da’irorin “da’irorin guguwa.” 14 Kowane daga kerubobin yana da fuskoki huɗu. Fuska ɗaya na kerub ne, na biyun fuskar mutum ne, na ukun fuskar zaki ne, na huɗun kuwa fuskar gaggafa ce.
15 Sai kerubobin suka tashi sama. Waɗannan ne halittu masu ran da na gani kusa da Kogin Kebar. 16 Sa’ad da kerubobin suka motsa, sai da’irorin da suke kusa da su su motsa; kuma sa’ad da kerubobin suka buɗe fikafikansu don su tashi daga ƙasa, da’irorin ba sa barin wurarensu. 17 Sa’ad da kerubobin suka tsaya cik, su ma sukan tsaya cik; kuma sa’ad da kerubobin suka tashi, sai su ma su tashi tare da su, domin ruhun rayayyun halittun yana a cikinsu.
18 Sai ɗaukakar Ubangiji ya tashi daga bisa madogarar ƙofar haikali ya kuma tsaya a bisa kerubobi. 19 Yayinda nake duba, kerubobin suka buɗe fikafikansu suka kuma tashi daga ƙasa, yayinda suka tafi kuwa, da’irorin suka tafi tare da su. Suka tsaya a mashigin ƙofar gabas na gidan Ubangiji, ɗaukakar Allah na Isra’ila kuwa yana a kansu.
20 Waɗannan ne rayayyun halittun da na gani a ƙarƙashin Allah na Isra’ila kusa da Kogin Kebar, na kuma gane cewa su kerubobi ne. 21 Kowanne yana da fuskoki huɗu da fikafikai huɗu, a ƙarƙashin kuwa akwai wani abin da ya yi kamar hannuwan mutum. 22 Fuskokinsu suna da kamanni ɗaya da waɗanda na gani kusa da Kogin Kebar. Kowanne ya tafi kai tsaye sosai.
11:1 Sa’an nan Ruhu ya ɗaga ni sama ya kawo ni ƙofar gidan Ubangiji wadda take fuskantar gabas. Can a mashigi zuwa ƙofar akwai mutum ashirin da biyar, na kuma ga a cikinsu akwai Ya’azaniya ɗan Azzur da Felatiya ɗan Benahiya, shugabannin jama’a. 2 Ubangiji ya ce mini, “Ɗan mutum, waɗannan su ne mutanen da suke ƙulla mugunta suna kuma ba da muguwa shawara a cikin wannan birni. 3 Suna cewa, ‘Lokaci bai yi kusa da za a gina gidaje ba? Wannan birni yana tukunyar dahuwa, mu ne kuwa naman.’ 4 Saboda haka yi annabci a kansu; yi annabci, ɗan mutum.”
5 Sai Ruhun Ubangiji ya sauko a kaina, ya kuma faɗa mini in ce, “Ga abin da Ubangiji yana cewa, haka kuke cewa, ya gidan Isra’ila, amma na san abin da yake a zuciyarku. 6 Kun kashe mutane da yawa a wannan birni kuka kuma cika titunanta da gawawwaki.
7 “Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa gawawwakin da kuka zubar a can su ne naman, wannan birni kuwa ita ce tukunya, amma zan kore ku daga cikinta. 8 Kuna jin tsoron takobi, kuma takobi ne zan kawo muku, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. 9 Zan kore ku daga birnin in miƙa ku a hannuwan baƙi in kuma azabtar da ku. 10 Za ku mutu ta wurin takobi, zan kuma hukunta ku a iyakokin Isra’ila. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji. 11 Wannan birni ba za tă zama muku tukunya ba, ba kuwa za ku zama nama a cikinta ba; zan hukunta ku a iyakokin Isra’ila. 12 Za ku kuwa san cewa ni ne Ubangiji, gama ba ku bi ƙa’idodina ba balle ku kiyaye dokokina, amma kuka bi hanyoyin al’ummai kewaye da ku.”
13 Yanzu yayinda nake yin annabci, sai Felatiya ɗan Benahiya ya mutu. Sai na fāɗi rubda ciki na kuma yi kuka da babbar murya na ce, “Kash, Ubangiji Mai Iko Duka! Za ka hallaka raguwar Isra’ila ƙaƙaf ne?”
14 Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa, 15 “Ɗan mutum, ’yan’uwanka, ’yan’uwanka waɗanda suke danginka na cikinka da kuma dukan gidan Isra’ila su ne waɗanda mutanen Urushalima suka ce, ‘Su ne da nisa daga Ubangiji; an ba mu wannan ƙasa ta zama mallakarmu.’
16 “Saboda haka ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ko da yake na kore su zuwa cikin al’ummai na kuma warwatsa su cikin ƙasashe, duk da haka na zama wuri mai tsarki a gare su a ƙasashen da suka tafi.’
17 “Saboda haka, ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan tattaro ku daga al’ummai in kuma dawo da ku daga ƙasashen da aka warwatsa ku, zan kuwa sāke mayar muku da ƙasar Isra’ila.’
18 “Za su dawo gare ta su kawar da dukan mugayen siffofi da gumaka masu banƙyama. 19 Zan ba su zuciya ɗaya in kuma sa sabon ruhu a cikinsu; zan fid da zuciyar dutse daga gare su in kuma ba su zuciya ta nama. 20 Sa’an nan za su bi ƙa’idodina su kuma yi hankali ga kiyaye dokokina. Za su zama mutanena, ni kuwa zan zama Allahnsu. 21 Amma game da waɗanda zukatansu suka karkata ga bin mugayen siffofi da gumakan banƙyama, zan sāka musu gwargwadon ayyukansu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”