An Dakatar da Shirin Mai da Yesu Sarki
An hana wani shirin juyin juya hali na ayyana Yesu a matsayin sarki (Almasihu na siyasa).
29 ko 28 bayan haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
Mattiyu 14:22–23
14:22 Nan da nan Yesu ya sa almajiran su shiga jirgin ruwa su sha gabansa, su haye zuwa ɗayan hayin, yayinda shi kuma yă sallami taron.
23 Bayan ya sallame su, sai ya haura bisan gefen dutse shi kaɗai don yă yi addu’a. Da yamma ta yi, yana can shi kaɗai,
Markus 6:45–46
6:45 Nan da nan Yesu ya sa almajiransa su shiga jirgin ruwa, su sha gabansa zuwa Betsaida, shi kuma yă sallami taron.
46 Bayan ya bar su, sai ya hau kan dutse don yă yi addu’a.
Yohanna 6:14–15
6:14 Bayan mutanen suka ga abin banmamakin da Yesu ya yi, sai suka fara cewa, “Lalle, wannan shi ne Annabin nan mai zuwa duniya.”
15 Da Yesu ya gane suna shirin su ɗauke shi ƙarfi da yaji su naɗa shi sarki, sai ya sāke komawa kan dutsen shi kaɗai.
Kiristi Ya Zo Wurin Sha Biyun a kan Ruwa
Sha biyun suna cikin haɗari a cikin guguwa a teku, Kiristi kuma ya zo wurinsu a kan ruwa cikin duhu.
Mattiyu 14:24–33
14:24 jirgin ruwan kuwa ya riga ya yi nesa da gaci, yana fama da raƙuman ruwa domin iska tana gāba da shi.
25 Wajen tsaro na huɗu na dare, sai Yesu ya nufe su, yana takawa a kan tafkin.
26 Sa’ad da almajiran suka gan shi yana takawa a kan tafkin, sai tsoro ya kama su. Suka yi ihu don tsoro suka ce, “Fatalwa ce.”
27 Amma nan da nan Yesu ya ce musu, “Ku yi ƙarfin hali! Ni ne. Kada ku ji tsoro.”
28 Sai Bitrus ya amsa ya ce, “Ubangiji in kai ne ka ce mini in zo wurinka a kan ruwan.”
29 Ya ce, “Zo.”
Sai Bitrus ya fita daga jirgin ruwan, ya taka a kan ruwan ya nufe wajen Yesu. 30 Amma da ya ga haukar iskar, sai ya ji tsoro, ya kuma fara nutsewa, sai ya yi ihu ya ce, “Ubangiji, ka cece ni!”
31 Nan da nan Yesu ya miƙa hannu ya kamo shi ya ce, “Kai mai ƙarancin bangaskiya, don me ka yi shakka?”
32 Da suka hau jirgin ruwan, sai iskar ta kwanta. 33 Waɗanda suke cikin jirgin ruwan kuwa suka yi masa sujada, suna cewa, “Gaskiya kai Ɗan Allah ne.”
Markus 6:47–52
6:47 Da yamma ta yi, jirgin ruwan yana tsakiyar tafkin, Yesu kuma yana can a ƙasa shi kaɗai.
48 Ya ga almajiran suna fama da tuƙi saboda iska tana gāba da su. Wajen tsara ta huɗu na dare, sai ya tafi wurinsu, yana takawa a kan tafkin. Ya yi kamar zai wuce su,
49 amma da suka gan shi yana takawa a kan tafkin, sai suka yi tsammani fatalwa ce. Sai suka yi ihu, 50 domin dukansu sun gan shi, suka kuma tsorata.
Nan da nan ya yi magana da su ya ce, “Ku yi ƙarfin hali! Ni ne. Kada ku ji tsoro.”
51 Sai ya shiga jirgin ruwan tare da su, iskar kuma ta kwanta. Dukansu suka yi mamaki, 52 gama ba su fahimci al’amarin burodin nan ba, don zuciyarsu ta taurare.
Yohanna 6:16–21
6:16 Da yamma ta yi, sai almajiransa suka gangara zuwa tafki,
17 inda suka shiga jirgin ruwa suka tasar wa haye tafkin zuwa Kafarnahum. A lokacin kuwa duhu ya yi, Yesu kuma bai riga ya zo wurinsu ba tukuna. 18 Iska mai ƙarfi kuwa tana bugowa, ruwaye kuma suka fara hauka.
19 Bayan sun yi tuƙi wajen mil uku ko uku da rabi, sai suka ga Yesu ya kusato jirgin ruwan, yana takawa a kan ruwan; sai suka tsorata. 20 Amma ya ce musu, “Ni ne; kada ku ji tsoro.”
21 Sa’an nan suka yarda suka karɓe shi a cikin jirgin ruwan, nan da nan kuwa jirgin ya kai gaɓar da za su.
An Marabci Yesu a Gennesaret
Mattiyu 14:34–36
14:34 Sa’ad da suka haye, sai suka sauka a Gennesaret.
35 Da mutanen wurin suka gane da Yesu, sai suka kai labari a ko’ina a ƙauyukan da suke kewaye. Mutane suka kawo masa dukan marasa lafiyarsu 36 suka kuwa roƙe shi yă bar marasa lafiya su taɓa ko da gefen rigarsa kawai, duk waɗanda suka taɓa shi kuwa suka warke.
Markus 6:53–56
6:53 Da suka haye, sai suka sauka a Gennesaret, suka daure jirgin a ƙugiya. 54 Da fitowarsu daga jirgin, sai mutane suka gane Yesu. 55 Suka gama yankin da gudu, suna ɗaukan marasa lafiya a kan tabarmai zuwa duk inda suka ji yake.
56 Duk inda ya shiga, cikin ƙauyuka, birane ko karkara, sai su kwantar da marasa lafiya a bakin kasuwa. Suka roƙe shi yă bari su taɓa gefen rigarsa kawai, kuma duk waɗanda suka taɓa shi kuwa, suka warke.